Annobar Coronavirus: Yan majalisun Kaduna sun bayar da makudan kudade don taimaka ma jama’a

Annobar Coronavirus: Yan majalisun Kaduna sun bayar da makudan kudade don taimaka ma jama’a

Kafatanin yayan majalisar dokokin jahar Kaduna sun amince da sadaukar da albashinsu na watan Afrilu domin yaki da cutar Coronavirus tare da rage ma al’ummar jahar radadin halin da cutar ta saka su a ciki.

Mataimakin kaakakin majalisar dokokin jahar, Muktar Isah Hazo ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 8 ga watan Afrilu dake dauke da sa hannunsa, inda yace yan majalisar jahar su 34 sun yanke shawarar sadaukar da albashinsu don jama’ansu.

KU KARANTA: Allah Ya kubutar da hadimin gwamnan jahar Nassarawa daga hannun masu garkuwa

Sanarwar ta kara da cewa yan majalisar sun dauki wannan

Annobar Coronavirus: Yan majalisun Kaduna sun bayar da makudan kudade don taimaka ma jama’a
Annobar Coronavirus: Yan majalisun Kaduna sun bayar da makudan kudade don taimaka ma jama’a
Asali: UGC

mataki ne domin taimaka ma kokarin da gwamnatin jahar Kaduna take yi na bayar da tallafin kayan abinci ga gajiyayyu da marasa karfi a jahar Kaduna.

Daga karshe sanarwar ta bayyana cewa kaakakin majalisar, Yusuf Zailani ya jinjina ma yan majalisa bisa sadaukarwar da suka nuna, sa’annan ya yi kira ga jama’an jahar su cigaba da kauce ma shiga taron jama’a don kiyaye kansu da kare yaduwar cutar, kamar yadda gwamnatin ta bukata.

A wani labarin kuma, wani mutumi da ba’a tabbatar da sunansa ba ya yanke jiki ya fadi a babbar kasuwar Igbudu dake garin Warri, ta karamar hukumar Warri ta kudu a jahar Delta, inda kuma ya mutu har lahira.

Punch ta ruwaito da misalin karfe 9 na safiyar Laraba ne mutumin ya tafi kasuwar da nufin siyayyar kayan abinci da kayan miya a lokacin da ajalinsa ya tarar da shi a can.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa: “Mutumin ya tafi kasuwar ne domin sayen kayan abinci, bayan ya sayi su tumatir da tarugu sai ya nemi inda zai sayi kifi danye, a nan wani mutumi ya nuna masa inda ake sayar da danyen kifi.

“Ya nufi inda ake sayar da danyen kifin kenan sai ya yanke jiki ya fadi ya mutu, mai yiwuwa ne mutumin ya mutu ne sakamakon yunwa, saboda ko daga tafiyarsa ya yi kama da mutumin da ya kwashe tsawon kwanaki bai ci abinci ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel