Za mu dawo da yan Najeriya, amma sai sun yi gwajin Coronavirus – hadimar shugaban kasa
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a shirye take ta kwaso yan Najeriya mazauna kasashen waje zuwa gida Najeriya, amma fa sai an yi musu gwajin Coronavirus, kuma an tabbatar basu dauke da ita.
Punch ta ruwaito gwamnatin ta bayyana haka ne a shafinta na yanar gizo inda ta nemi yan Najeriya mazauna kasashen waje su bayar da bayani game da matsayin lafiyarsu dangane da cutar Coronavirus, musamman ga duk masu son a dawo dasu Najeriya.
KU KARANTA: Yayan gwamnan jahar Bauchi ya fito daga hannun masu garkuwa da mutane
“Dole sai an yi musu gwajin cutar a kasar da suke zama, kuma an basu takarda a hukumance dake tabbatar da basu dauke da cutar, dole ne su gabatar da wannan takarda a filin jirgi domin a tabbatar da sahihancinsa kafin a kyalesu su shiga cikin jirgi.
“Haka zalika duk mai son ya dawo gida shi da kansa zai biya kudin jirgi, sa’annan da zarar an sauka a Najeriya za’a killace mutum tsawon kwanaki 14 a duk inda hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta ga ya dace.” Inji sanarwar.
Da take tabbatar da batun, mashawarciyar shugaban kasa a kan harkokin kasashen waje, kuma shugabar hukumar dake kula da sha’anin yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri Erewa ta bayyana cewa hakan na cikin tsarin NCDC, kuma dole ne a bi shi.
A wani labarin kuma, wata mata yar Najeriya mai shekaru 64 a duniya Mmaete Greg ta rasu a kasar Birtaniya sakamakon kamuwa da ta yi da cutar Coronavirus, kamar yadda gwajin da aka gudanar a kanta ya tabbatar.
Mmaete wanda mazauniyar garin Landan ce ta mutu ne a ranar Litinin, 6 ga watan Maris, kamar yadda wani dan uwanta Edoamaowo Udeme ya tabbatar ma manema labaru, kuma ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Udeme ya bayyana cewa mamaciyar tana zama ne a Birtaniya, kuma a can take aiki, inda ta kwashe sama da shekaru 40 a hukumar Yansandan birnin Landan, daga bisani ta yi ritaya da kan ta.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng