Ya yanke jiki ya fadi: Magidanci ya mutu yayin da yake cinikin sayen kayan abinci
Wani mutumi da ba’a tabbatar da sunansa ba ya yanke jiki ya fadi a babbar kasuwar Igbudu dake garin Warri, ta karamar hukumar Warri ta kudu a jahar Delta, inda kuma ya mutu har lahira.
Punch ta ruwaito da misalin karfe 9 na safiyar Laraba ne mutumin ya tafi kasuwar da nufin siyayyar kayan abinci da kayan miya a lokacin da ajalinsa ya tarar da shi a can.
KU KARANTA: Yayan gwamnan jahar Bauchi ya fito daga hannun masu garkuwa da mutane
Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa: “Mutumin ya tafi kasuwar ne domin sayen kayan abinci, bayan ya sayi su tumatir da tarugu sai ya nemi inda zai sayi kifi danye, a nan wani mutumi ya nuna masa inda ake sayar da danyen kifi.
“Ya nufi inda ake sayar da danyen kifin kenan sai ya yanke jiki ya fadi ya mutu, mai yiwuwa ne mutumin ya mutu ne sakamakon yunwa, saboda ko daga tafiyarsa ya yi kama da mutumin da ya kwashe tsawon kwanaki bai ci abinci ba.” Inji shi.
Amma ko da aka tuntubi hukumar Yansandan jahar Delta domin jin ta bakinsu game da lamarin, sai jami’in dake magana da yawunta, Onome Onovwakpoyeya yace tabbas lamarin ya auku.
“Da gaske ne, amma bamu san abin da ya yi sanadiyyar ajalinsa ba, saboda mu ba likitoci bane, mutumin ya dai yanke jiki ya fadi ya mutu kawai.” Inji shi.
A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jahar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi kira ga gwamnatoci, kungiyoyin addinai, kamfanoni masu zaman kansu da kuma masu hannu da shuni da su mayar da hankali wajen tallafa ma jama’a da kayan abinci.
Gwamnan ya bayyana haka ne a garin Ado Ekiti ta bakin mai magana da yawunsa, Lere Olayinka, inda ya yi kira ga wadanda abin ya shafa da su dauki shawararsa da muhimmanci.A cewar tsohon gwamnan, yunwa ta fi Coronavirus kashe yan Najeriya, kuma ta fi kisa cikin sauri.
Sa’annan ya kara da cewa za’a yi fama da matsalolin tattalin arziki da ire irensu a sanadiyyar bullar Coronavirus, don haka yanzu ne ya kamata shuwagabanni su tashi tsaye su nuna jagoranci nagari ga al’ummarsu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng