An sako shahararren dan wasan kwallon kafa Ronaldinho daga gidan yari

An sako shahararren dan wasan kwallon kafa Ronaldinho daga gidan yari

- An sako babban da wasan kwallon kafa na kasar Brazil, Ronaldinho daga gidan yarin Paraguay

- Tun a ranar 6 ga watan Maris ne aka garkame tsohon dan wasan kwallon kafan a gidan yari sakamakon fasfotin bogi da ya mallaka

- Ronaldinho ya kwashe kwanaki 32 ne a gidan yarin tare da dan uwan shi Roberto de Assis sakamakon yunkurin shiga Paraguay da suka yi

An sako babban dan kwallon kafa na kasar Brazil, Ronaldinho, daga gidan yarin Paraguay inda aka tsare shi na kwanaki 32 bayan an zarge shi da mallakar fasfotin bogi.

Tsohon tauraron kungiyar kwallon kafa ta Barcelonan, wanda ya yi nasarar cin kofin duniya na gasar kwallon kafa a 2002, an bada umarnin garkame shi ne tare da dan uwanshi a otal din Palmaroga da ke Asuncion.

An sako shahararren dan wasan kwallon kafa Ronaldinho daga gidan yari

An sako shahararren dan wasan kwallon kafa Ronaldinho daga gidan yari
Source: Instagram

An garkame Ronaldinho tare da dan uwanshi Roberto de Assis ne a ranar 6 ga watan Maris bayan sun shiga kasar Paraguay da fasfotin bogi.

DUBA WANNAN: Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji

Fastotin kasar Paraguay din da aka samu a tare dasu masu sunan Ronaldinho da Roberto sun bada matukar mamaki don an kwace fasfotinsu na kasar Brazil a shekarar 2018 bayan wani laifi da suka aikata.

Ya sanar da hukumomi a wani faifan murya, cewa wadannan takardun kyauta ne garesu daga wani dan kasuwar kasar Brazil din mai suna Wilmondes Sousa Liria, wanda shima aka garkame.

A yayin yanke hukunci, Mai shari’a Gustavo Amarilla ya ce: “Na yanke shawarar garkamesu a gida ne saboda an samu bincike mabanbanci da na wata daya da ya gabata.”

Lauyan Ronaldinho, Adolfo Marin ya ce tsohon dan kwallon kafan bai kyauta ba kuma an kalubalance shi saboda bai amsa laifinsa a gaban kotu ba.

“Kotun ba ta duba cewa Ronaldinho bai san ya yi laifi ba saboda bai san cewa takardun bogi ne aka bashi ba,” A cewar lauyan.

Idan aka yanke wa tsohon dan wasan hukunci, akwai yuwuwar ya kwashe shekaru biyar a gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel