COVID-19: FRSC ta kama mutum 321 da suka karya dokar takaita zirga-zirga

COVID-19: FRSC ta kama mutum 321 da suka karya dokar takaita zirga-zirga

- Hukumar kula da hadurra ta ce an kama masu laifi 321 sakamakon take dokar hana walwala da suka yi

- An kama jama’ar ne a fadin jihohin kasar nan sakamakon laifuka daban-daban da suka aikata

- Ya shawarci fasinjoji da kada su amince direbobi na saka su kamar kifi cikin mota gudun yaduwar cutar coronavirus

Hukumar kula da hadurra ta tarayya ta ce an kama masu laifi 321 sakamakon take dokar hana walwala da suka yi a wasu jihohin kasar nan.

Jami’in wayar da kai na FRSC, Bisi Kazeem, ya bayyana hakan ne a wata takarda da ta fita a ranar Talata. Ya ce an yi kamen ne daga ranar 30 ga watan Maris zuwa 6 ga watan Afirilu.

COVID-19: An kama mutum 321 da suka karya dokar takaita hana zirga-zirga
COVID-19: An kama mutum 321 da suka karya dokar takaita hana zirga-zirga
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji

Kamar yadda gidan talabijin din Channels ya bayyana, an kama wadanda ake zargin ne sakamakon laifuka daban-daban da suka hada da daukar fasinjoji masu yawa a mota da kuma take dokar nisantar juna don hana yaduwar cutar coronavirus.

Shugaban hukumar, Boboye Oyeyemi, ya yi kira ga masu ababen hawa da su guji zuba jama’a masu yawa a ababen hawa.

Ya kara da jan kunnen fasinjoji da su guji hawa abun hawa wanda ya kwashi mutane masu tarin yawa.

Kamar yadda Oyeyemi ya sanar, dole ne kowa ya kiyaye dokokin kiwon lafiya don take su yana da matukar hatsari. Hakan kuma zai iya kawo barkewar cutar coronavirus wanda ba a fata.

A wani labarin, kun ci cewa mazauna unguwar Narayi a garin Kaduna sun yi warwason kayan abincin da aka ajiye da niyyar raba wa marasa karfi a unguwa yayinda yan kwamitin da aka daura wa alhakin rabon kayan abincin suka zuba musu ido suna kallonsu babu yadda za su yi da su.

Kamfanin Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ne ta bayar da kayayyakin abincin domin a raba wa talakawa yayin da suke zaune a gidajensu sakamakon dokar hana fita da aka saka saboda coronavirus.

Shugaban kwamitin rabon, Malam Sule Garba ya ce lamarin ya afku ne a ranar Litinin da yamma a makarantar frimari ta LEA da ke Narayi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Garba wanda kuma shine mai unguwar ta Narayi, ya shaidawa NAN a ranar Talata a Kaduna cewa dandazon matasa maza da mata sun suke wawushe kayin abincin suka tsere.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel