Gwamnatin jihar Nasarawa za ta mayar da almajiran jihar gaban iyayensu

Gwamnatin jihar Nasarawa za ta mayar da almajiran jihar gaban iyayensu

- Gwamna Sule na jihar Nasarawa ya ce yana kokarin mayar da almajirai gaban iyayensu

- Kamar yadda ya bayyana, malaman tsangaya ne za su jagoranci wannan komen don sun fi kowa sanin asalin almajiran

- Kamar yadda sarkin Lafia, Jastis Sidi Dauda Bage mai murabus ya ce akwai bukatar fara kwashe yaran da gaggawa don saduwa da iyayensu

Gwamna Sule na jihar Nasarawa ya ce yana kokarin mayar da almajiran jihar asalin jihohinsu.

Ya sanar da hakan ne a yayin da yake samun rahoton kwamitin da ya kafa don taimakon gwamnati wajen mayar da almajiran asalin jihohinsu.

Gwamna Sule ya ce, "Za a mayar da almajiran gaban iyayensu ne daki-daki kuma tare da hadin guiwar gwamnonin jihohinsu. Malaman tsangaya za su jagoranci yaran nan har zuea gaban iyayensu, komai kuwa nisansu don tabbatar da cewa an kaisu gaban iyayensu,"

A jawabin sarkin Lafia, Jastis Sidi Dauda Bege mai ritaya, ya ce rahoton na bukatar aikin gaggawa wajen kwashe yaran masu shekaru kasa da 10 don komawa gaban iyayensu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

"Bayan an kammala na masu shekaru 10, sauran za a duba su. Akwai wasu sharudda da dole kowanne almajiri ya cika kafin a bar shi ya zauna a jihar," yace.

Gwamnatin jihar Nasarawa za ta mayar da almajiran jihar gaban iyayensu
Gwamnatin jihar Nasarawa za ta mayar da almajiran jihar gaban iyayensu
Asali: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Za mu gwada amfani da magungunan gargajiya - Ministan lafiya

A wani labari na daban, Wasu 'yan Najeriya mazauna kasar China sun zargi 'yan kasar da fatattakarsu daga dakunan otal don gudun kada su dawo musu da cutar coronavirus.

Kwayar cutar dai ta samo asali ne daga garin Wuhan na kasar China din inda ya zama annoba ga dukkan duniya. A halin yanzu kuwa ya kama a kalla mutane miliyan daya a fadin duniya.

Wani bidiyo sabo mai cike da abun mamaki na yadda ake tsangwamar 'yan Najeriya a kasar Chinan ya yawaita a kafafen sada zumuntar zamani.

A bidiyon, an ga 'yan sandan kasar Chinan na korar 'yan kasuwar Najeriya daga dakin otal.

An ji 'yan Najeriyan suna cewa 'yan sandan Chinan, akwai 'yan kasarsu da ke yadda suka so a dukkan kasashen Afrika ba tare da tsangwama ba. Mutanen sun kara da cewa ai kasar China ce ta kawo kwayar cutar har ta shafi 'yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel