Tallafin man fetur: Kyari ya yi bayani game da janye tallafi da FG tayi

Tallafin man fetur: Kyari ya yi bayani game da janye tallafi da FG tayi

Zamanin tallafin man fetur ya tafi har abada, manajan daraktan NNPC, Mele Kyari ya sanar da hakan a ranar Litinin.

Kyari, wanda ya yi magana kai tsaye da gidan talabijin din AIT, ya ce da irin hawa da sauka da ake samu na farashin man fetur, kudin tatattun kayayyakin man fetur ba za su daidaita ba har sai an ga abinda kasuwa ta nuna.

Ya bayyana cewa, duk da cewa NNPC ba ta da alhakin fitar da farashin kayayyakin man fetur, kasar tana kokarin komawa wani salo na siyar da fetur ne.

Tana so yanayin bukata da samuwar man fetur su kasance madogara a farashin shi.

A watan Maris, gwamnatin tarayya ta rage farashin litar man fetur daga N145 zuwa N125.

A ranar daya ga watan Afirilu, farashin litar man fetur din ya gangara zuwa N123.50 duk da kuwa daukacin 'yan Najeriya na tsammanin farashin ya gangara kasa da hakan.

Hukumar daidaita farashin kudin kayayyakin man fetur ta yi bayanin cewa, ragowar farashin litar ya faru ne sakamakon faduwar farashin danyen man fetur a duniya saboda barkewar annobar coronavirus.

A lokacin da aka sanar da shi cewa 'yan Najeriya na tsammanin raguwar farashin man fetur din fiye da haka, Kyari ya yi bayanin cewa akwai dalilai masu tarin yawa da ke kawo ragowa a farashin.

Tallafin man fetur: Kyari ya yi bayani game da janye tallafi da FG tayi
Tallafin man fetur: Kyari ya yi bayani game da janye tallafi da FG tayi
Asali: UGC

KU KARANTA: Wata sabuwa: Cutar Coronavirus na dawowa jikin mutanen da aka yi musu magani, yayin da ta dawo jikin mutane 51 da suka warke a kasar Koriya ta Kudu

Ya ce: "Na san muna kokarin komawa tsari ne wanda yanayin bukata da samuwar man fetur din ne zai daidaita farashin shi. A don haka ne na san cewa kasuwa ce kadai za ta fdaidaita arashin ta yadda kowa zai ji dadi."

Ya ce faduwar farashin danyen man fetur din zai bayyana ne har a kan sauran kayayyakin da ake samu daga danyen man fetur din nan da makonni hudu.

Kyari ya ce, "Bana tsammanin gangar danyen man fetur za ta fadi kasa da dala 20 kamar yadda muka gani a makon da ya gabata. Ina da tabbacin cewa farashin danyen man fetur zai koma yadda yake."

Ya ce NNPC na fatan samar da danyen man fetur har ganga miliyan uku a rana daya.

Ya ce"Daga jiya, yanayin samar da man fetur dinmu ya karu har zuwa ganga miliyan 2.3. Lamarin da ya shafe watanni ko kuma shekaru bai faru ba."

Ya bayyana cewa hakan suke fatan ya ci gaba da faruwa har a kai ga inda ake so.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel