COVID-19: Za mu gwada amfani da magungunan gargajiya - Ministan lafiya
- Ministan Lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire ya ce gwamnatin tarayya za ta fara duba masu ruwa da tsaki a fannin magungunan gargajiya don yakar cutar coronavirus a kasar nan
- Ministan ya sanar da hakan ne a taron manema labarai da yayi tare da kwamitin shugaban kasar na yaki da cutar coronavirus wanda aka yi a Legas a ranar Talata
- Ministan ya ce gwamnatin tarayya tana kara dogaro ne da cibiyar kiwon lafiya ta duniya kamar dai yadda sauran kasashe ke yi don gano ingantaccen maganin muguwar cutar
Ministan Lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire ya ce gwamnatin tarayya za ta fara duba masu ruwa da tsaki a fannin magungunan gargajiya don yakar cutar coronavirus a kasar nan.
Ministan ya sanar da hakan ne a taron manema labarai da yayi tare da kwamitin shugaban kasar na yaki da cutar coronavirus wanda aka yi a Legas a ranar Talata.
Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, ya ce za a duba a ga manyan masu maganin gargajiya da ke amfani da tsumi, sassake da dauri don gwaji.
KU KARANTA: Wata sabuwa: Cutar Coronavirus na dawowa jikin mutanen da aka yi musu magani, yayin da ta dawo jikin mutane 51 da suka warke a kasar Koriya ta Kudu
"Za mu duba ta kowanne bangare ne da niyyar samun mafita. Wasu suna cewa suna da maganin gargajiya da zai kashe cutar. Wadanda suka mayar da hankali kadai ma'aikatar lafiya za ta saurari ikirarinsu kuma ba za mu gwasale su ba," yace.
"Za mu duba ingancin magungunan gargajiyan kafin mu aminta da shi don amfanin jama'a." Ya ce.
Ya kara da cewa, za a yi gwaji mai tarin yawa kafin a a tabbatar da maganin sannan a fitar.
"Kamar abinda ya faru da hydroxychloroquine wanda aka samu yana aiki a waje amma ba a jikin dan Adam ba. Dole ne kuwa a tantance magungunan gargajiya da kuma gano illolinsu," yace.
Ministan ya ce gwamnatin tarayya tana kara dogaro ne da cibiyar kiwon lafiya ta duniya kamar dai yadda sauran kasashe ke yi don gano ingantaccen maganin muguwar cutar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng