Tashin hankali: Wani dan Najeriya mai Coronavirus ya gantsarawa ma'aikaciyar jinya cizo a fuska

Tashin hankali: Wani dan Najeriya mai Coronavirus ya gantsarawa ma'aikaciyar jinya cizo a fuska

Jami'an tsaro sun garkame wani dan Najeriya mai fama da cutar Coronavirus kan laifin gantsarawa wata ma'aikaciyar jinya yar kasar Sin cizo a fuska don ta hanashi guduwa daga inda aka killaceshi.

Mutumin mai suna Okonkwonwoye Chika Patrick ya doki matar ne saboda bayan ta hanashi fita daga asibitin dake Guwangzhou.

Faifan bidiyon ya nuna yadda ma'aikaciyar jinyar tana fashewa da kuka tana nuna wuraren da ya ji mata rauni.

Tashin hankali: Wani dan Najeriya mai Coronavirus ya gantsarawa ma'aikaciyar jinya cizo a fuska

Tashin hankal
Source: Facebook

Yayinda ta bukaci daukar jininsa domin yin gwaji ranar 1 ga Afrilu, Okonkwonwoye yayi banza da ita kuma ya nufi fita daga dakin killacewar.

Yayinda tayi kokarin tareshi daga fita, sai ya ture ta kasa, ya cijeta a fuska.

Jami'an yan sanda sun garkameshi kuma yana cigaba da jinya karkashin lurar yan sanda. Za'a hukuntashi bisa dokokin kasar Sin lokacin da ya samu lafiya.

Dan Najeriyan, Okonkwonwoye Chika Patrick, ya kasance a asibitin tun ranar 23 ga Maris, 2020.

Ya kamu da cutar Coronavirus bayan komawa garin Guangzhou ranar 20 ga Maris.

Kalli bidiyon ma'aikaciyar jinyar:

KU KARANTA: Covid19: Yadda mutane suka yi wawaso wurin rabon tallafin kayan abinci a Kaduna

A nan gida kuwa, Mazauna unguwar Narayi a garin Kaduna sun yi wawason kayan abincin da aka ajiye da niyyar raba wa marasa karfi a unguwa a suka bar yan kwamitin da aka daura wa alhakin rabon kayan abincin sun kallonsu babu yadda za su yi da su.

Kamfanin Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ne ta bayar da kayayyakin abincin domin a raba wa talakawa yayin da suke zaune a gidajensu sakamakon dokar hana fita da aka saka saboda coronavirus.

Shugaban kwamitin rabon, Malam Sule Garba ya ce lamarin ya afku ne a ranar Litinin da yamma a makarantar frimari ta LEA da ke Narayi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Garba wanda kuma shine mai unguwar ta Narayi, ya shaidawa NAN a ranar Talata a Kaduna cewa dandazon matasa maza da mata sun suke wawushe kayin abincin suka tsere.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel