COVID-19: Dalilin da yasa wasu mutane ke warkewa da gaggawa - Farfesa Otegbayo

COVID-19: Dalilin da yasa wasu mutane ke warkewa da gaggawa - Farfesa Otegbayo

Shugaban likitoci na asibitin koyarwa na jami'ar Ibadan, Farfesa Jesse Otegbayo, ya bayyana dalilin da yasa mutane ke warkewa daga cutar coronavirus cikin kwanaki kalilan.

A yayin jaddada wannan ci gaban, ya ce mutane bai kamata su dinga mamakin hakan ba. Otegbayo ya ce akwai wasu abubuwan da suka hada da tsohuwa cuta, karfin garkuwar jiki da kuma kwayar cuta jiki yana tantance kwanakin da kwayar cutar ke yi a jiki.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da yayi da jaridar The Nation a kan yadda killace kai ke faruwa.

Shugaban asibitin dai a makon da ya gabata ne ya bayyana baya dauke da cutar bayan a ya dau kwanaki takwas yana jinyar cutar.

COVID-19: Dalilin da yasa wasu jama'a ke warkewa da gaggawa - Farfesa Otegbayo
COVID-19: Dalilin da yasa wasu jama'a ke warkewa da gaggawa - Farfesa Otegbayo
Asali: UGC

Shugaban asibitin ya yi bayanin cewa kwayar cutar ya fi illata masu tsohuwar cuta irinsu daji, ciwon zuciya, ciwon sukari da sauransu. Ya kara da cewa masu garkuwar jiki mara karfi sun fi fuskantar matsala babba idan kwayar cutar ta shiga jikinsu.

DUBA WANNAN: Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji

Ya ce: "Warkewar da nayi daga cutar cikin kwanaki kalilan ya faru ne sakamakon garkuwar jiki na. Wasu garkuwar jikinsu bata da karfi. A misali, idan mutum na yin mura kuma yana tari, wasu mutane na iya yin mu'amala dasu ba tare da sun kwashi cutar ba. Wasu kuwa babu dadewa suke dibar cutar."

Ya kara da cewa, "masu ciwuka da ke nan a jikinsu na iya faduwa saboda kwayar cutar. Idan mutum yana dauke da cutar daji, ciwon zuciya ko kuma ciwon sikafi, akwai yuwuwar garkuwar jikinsu ta zama mara karfi."

Otegbaya ya ce, bai dace mutanen da suka warke daga cutar ba su koma aiki da gaggawa ko kuma su fara mu'amala da jama'a ba. Hakan yana daga cikin abubuwan da cibiyar kula da cutuka masu yaduwa ta sanar.

"Ga wadanda suka warke daga cutar, ya kamata su gaggauta bin dokokin NCDC. Bayan gwaji na biyu, ana zaunawa a gida ne ba tare da an je aiki ba na kwanaki bakwai. Duk wadanda suka karya wannan dokar na karya dokokin kiwon lafiya ne," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel