Yanzu-yanzu: An sallami mutane 7 daga asibiti a Abuja bayan sun warke daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 7 daga asibiti a Abuja bayan sun warke daga Coronavirus

- Tabarkallah! Mutane bakwai sun samu waraka daga cutar Coronavirus a birnin tarayya Abuja

- Ana kyautata zaton cewa cikinsu akwai dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar

Mutane bakwai dake killace a asibitin jamiar Abuja bayan sun kamu da cutar Coronavirus a makonni baya sun samu lafiya kuma an sallamesu.

Ministan birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, ya bayyana hakan ne ranar Talata.

Yace “Tun lokacin da cutar COVID-19 ta bulla a birnin tarayya, ina samun labarin halin da marasa lafiyan ke ciki.“

“ Ina farin cikin sanar muku cewa mutanen farko da za a sallama, su bakwai, sun warke daga cutar bayan gwajin karshe da akayi musu.“

“Hakazalika, jajirtattun ma“aikatan kiwon lafiyanmu na iyakan kokarinsu wajen ganin cewa sauran marasa lafiya 39 sun samu lafiya.“

“Ina son tunawa mazauna Abuja cewa gwamnati na jaddada niyyarta na yakar wannan annobar.“

“Ko tattalin kudi ba za muyi ba wajen ganin cewa an takaita yaduwar cutar da kare rayuwar mutanenmu.“

Ministan ya kara da cewa mazauna Abuja sun yi biyayya ga umurnin hana zirga-zirga da shugaba Muhammadu Buhari yayi.

A yanzu, mutane 238 aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya. Yayinda 35 sun warke, ana rasa rayuka 5.

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 7 daga asibiti a Abuja bayan sun warke daga Coronavirus

Abuja
Source: Facebook

A wani labarin mai alaka, Jami'an tsaron tabbatar da dokar hana fita a birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin kwamishanan yan sandan FCT, Bala Ciroma, sun damke motoci 51, babura 46 da keken adaidata sahu 9, sakamakon saba doka.

Jami'an tsaron sun kwace wadannan ababen hawan ne daga hannun mammalakansu yayinda suka fito waje maimakon zamansu a gida kamar yadda shugaban kasa yayi umurni.

Kakakin hukumar yan sandan Abuja, DSP Anjuguri Manzah, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Asabar.

Ciroma ya ce an kama motoci, babura da kekunan adaidaita sahun ne a unguwannin Nyanya, Dutse Alhaji, Karu, Jabi, Kado, Life-camp, Mpape, Zuba, dss.

Ya ce ababen hawan zasu kasance hannun hukuma har sai wa'adin kwanaki 14 na dokar da gwamnatin tarayya ta sa ya shude.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel