Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutum daya bayan samun waraka daga COVID-19

Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutum daya bayan samun waraka daga COVID-19

Gwamnatin jihar Legas a ranar Alhamis ta sanar da kara sallamar wata mai fama da cutar Coronavirus daga asibitin jihar bayan kwashe kwanaki tana jinya.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewa an saki matar ne bayan gwaji biyu daban-daban sun nuna cewa ta barranta daga kwayar cutar.

Yace “Cikin farin cikin nike sanar muku cewa an sake sallamar mara lafiya (mace) wacce ta warke gaba daya a asibitinmu dake Yaba.“

“A yanzu mutane 32 kenan muka yi jinyarsu tare da sallamarsu a Legas.“

“Ina kyautata zaton cikin kwanaki masu zuwa zan cigaba da kawo muku labarai masu dadi“

“Wannan na nuna cewa matakan da muke dauka wajen yakar cutar COVID-19 na aiki kuma zamu cigaba da samun nasara.“

Kawo yanzu, mutane 36 sun samu waraka daga cutar Coronavirus a fadin tarayya.

A ranar Litinin, gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa mutane 84 suka rage a asibitinsu yanzu ana kula da su.

Gwamnan ya yi kira da yan jihar Legas su kasance masu biyayya ga dokar da shawarin masana kiwon lafiya musamman wajen rashin cudanya da izdihami.

Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutum daya bayan samun waraka daga COVID-19
waraka daga COVID-19
Asali: Twitter

A wani labarin daban, Biloniya a kasar China, Jack Ma, ya sake aiko da karin wasu kayan duba lafiya da suka hada da na'urar taimakon numfashi 500 zuwa kasashen Afrika 54 domin su yaki cutar covid-19.

Jack Ma, attajirin dan kasuwa, ya sanar da hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Ya bayyana cewa sauran kayan da ya bayar da tallafinsu sun hada da kayan sakawar ma'aikatan lafiya 200,000, takunkumin rufe fuska 200,000, na'urar sanin sanyi ko zafin jiki 2,000, safar hannu 500,000 da sauransu.

A baya, wannan attajiri ya aikowa Najeriya kayayyakin garkuwar jiki ga maaikatan kiwon lafiya domin gudanar da ayyukansu ba tare da tsoron kamuwa da cutar Coronavirus ba.

Hukumar NCDC ta raba wadannan kayayyaki ga jihohin Najeriya 36.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel