Covid19: Yadda mutane suka yi wawaso wurin rabon tallafin kayan abinci a Kaduna
Mazauna unguwar Narati a garin Kaduna sun yi wawason kayan abincin da aka ajiye da niyyar raba wa marasa karfi a unguwa yayinda yan kwamitin da aka daura wa alhakin rabon kayan abincin suka zuba musu idoo suna kallonsu babu yadda za su yi da su.
Kamfanin Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ne ta bayar da kayayyakin abincin domin a raba wa talakawa yayin da suke zaune a gidajensu sakamakon dokar hana fita da aka saka saboda coronavirus.
Shugaban kwamitin rabon, Malam Sule Garba ya ce lamarin ya afku ne a ranar Litinin da yamma a makarantar frimari ta LEA da ke Narayi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Garba wanda kuma shine mai unguwar ta Narayi, ya shaidawa NAN a ranar Talata a Kaduna cewa dandazon matasa maza da mata sun suke wawushe kayin abincin suka tsere.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji
Ya lissafa cewa kayayyakin sun kunshi katon 170 na taliyar spagetti, katon din Indomie 1,250, kananan jakunkuna da aka dauke da shinkafa mudu 650, wake mudu 230 da galan din man gyada 800.
Ya yi bayanin cewa saboda adalci da gudun zargi, kwamitin da sauke kayayyakin ne a makarantan LEA na Narayi jim kadan sai mata da yara suka cika wurin domin karbar rabon su.
Ya ce an fara samun matsala ne lokacin da yan kwamitin suka gaza cimma matsaya kan tsarin da za ayi amfani da shi wurin rabon kayan tallafin.
Mai unguwar ya ce ana cikin wannan hali ne sai wasu mutane suka fara daukan kayan abincin suna mika wa yan gidansu da abokansu.
Ya ce, "Muna cikin rabon kayan abincin daya bayan daya kwatsam sai mutanen suka fi karfin mu, kowa ya fara diban abinda hannunsa zai iya dauka.
"Mun yi iya kokarin mu amma sun mana yawa domin kowa cikin su yana son ya samu rabonsa ne ta ko wane hali."
Ya kara da cewa mambobin Kungiyar Sa Kai na Civilian JTF da ya kamata su basu tsaro su kuma taimaka wurin tabbatar da cewa mutanen sun bi tsari su ma suka shiga wawason domin samun rabonsu.
Garba ya ce, "Na gode wa Allah tunda ba bu wanda ya rasa ransa."
Da ya ke martani kan lamarin, shugaban Civilian JTF, Mista Silas Kuje ya ce bai da labarin cewa yan kungiyarsa sun shiga wawason amma ya ce zai yi bincike a kan zargin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng