Zamfara: Yan sanda samu sunayen mayan 'yan siyasar jihar a matsafa

Zamfara: Yan sanda samu sunayen mayan 'yan siyasar jihar a matsafa

- Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa ta samu sunayen manyan 'yan siyasar jihar rubuce a takarda a wata matsafa

- Kamar yadda kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Nagogo ya ce sun kai samame ne bayan bayanan sirri da suka samu

- Ya ce mazauna yankin sun ce a duk lokacin da matsafan suka fara surkullensu, kadangaru da sauran kananan dabbobi na yankin na mutuwa

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta ce ta samu sunayen manyan 'yan siyasar jihar rubuce a wata takarda a wani gidan tsafi a babban birnin jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Nagogo ne ya sanar da hakan a yau Talata bayan samamen da jama'arsa suka kai moboyar matsafan a Gusau.

Zamfara: An gano sunayen manyan 'yan siyasa a gidan boka

Zamfara: An gano sunayen manyan 'yan siyasa a gidan boka
Source: Twitter

Ya ce 'yan sandan sun samu sahihin bayanin sirri daga wasu mutane. Sun ce wasu manyan mutane da ke a karagar siyasar garin suna kokarin amfani da tsafi don kai hari.

Nagogo ya ce bayanin sirrin ta nuna cewa gidan tsafin na nan ne a Unguwar Dallatu da ke kusa da tashar mota. Kuma ana zuwa ne don tsafi.

DUBA WANNAN: Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji

Ya ce wadanda suka kai bayanan sun ce mazauna yankin sun gano cewa duk lokacin da matsafan suka shiga gidan, dukkan kananan halittu kamar sh kadangaru da kiyashi na mutuwa.

Rundunar 'yan sandan sun tsinkayi gidan ne da gaggawa amma ana ganin hasken wutar jami'an tsaron, sai matsafan suka fara surkullensu tare da hanzarta tserewa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce wasu daga cikin kayayyakin da aka samu daga matsafar sun hada da kwarya cike da jini, tukunya mai cike da allurai, Leda mai dauke da kaya kala daban-daban, kwarangwal din mutum da kuma takarda mai dauke da sunayen manyan 'yan siyasar jihar.

Nagogo ya ce ana ci gaba da binciken lamarin kuma za a sanar da jama'a kowanneci gaba dangane da hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel