Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji

Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji

Don samun nasara a yaki da annobar coronavirus, dole ne 'yan Najeriya su ajiye addini tare da rungumar ilimi, inji shugaban One Love Family, Sat Guru Maharaj Ji.

A yayin zantawa da manema labarai a garin Legas, Maharaj Ji ya ce hanya daya kuma mafita ga 'yan Najeriya ita ce amfani da sunan Ubangiji kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya ce, "Mun gano cewa kalmar Ubangiji bata da ma'ana kuma ana amfani da ita ne hana mutane morar albarka daga Ubangiji. Dole ne jama'a su bar addinai kwata-kwata sannan a samu mafita."

Ya kara da cewa, "Idan mutum ba bukatar aiki, babu amfanin kabila ko addini. Abu ne da ba za a iya hanawa ba, za a iya kafa shi. Coronavirus matacciya ce a duk lokacin da muka hada kai tare da rungumar juna."

Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji
Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Premium Times ta bayyana, Maharaj Ji ya ce, "kowa ya san cewa addinai ba za su iya maganin coronavirus ba. An rufe Saudi Arabia, Makka, Madina da kuma hanyoyi. A yanzu ina karfin Musa na raba ruwa biyu? Ina karfin Dawud? Babu abinda ya gagari Ubangiji. Rayuka na ta salwanta saboda rashin ilimi."

A ranar 6 ga watan Afirilu, masu cutar Coronavirus a Najeriya sun kai 238, an sallami mutane 35 daga asibiti inda mutane biyar suka rasa rayukansu.

DUBA WANNAN: Labari da dumi-dumi: Tsohon malamin da ya koyar da Abacha, Dr Habibu Gwarzo ya rasu a Kano

A watan da ya gabata, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya kamu da cutar coronavirus. An kuwa kai shi cibiyar killace mutane masu cutuka masu yaduwa ta Abuja inda daga bisani aka mayar dashi Legas.

A yayin zantawa da manema labarai, Maharaj Ji ya zargi shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar da yaudara. A don haka yayi kira da a hukunta shi.

"Ka je kasar waje har zuwa kasar China kuma kana sane da cewa akwai matsaloli. Ya kamata a ce ya killace kansa na kwanaki 14 amma ya ki yin hakan. Waye shi kuma meye burinsa?"

Ya kwatanta hana walwala da aka yi sassan kasar nan da lamari mai tsoratarwa. Ya kara da kira ga gwamnatin da ta samar da hanyoyin gwajin cutar a sassan fadin kasar nan.

"Ba mu san me ke faruwa a kasar China da Turai ba. Bamu san me suke cewa ba. Mu nemi hanyar yakar cutar nan. Ba za mu hada kanmu da wasu ba. Suna cin abinci ba irin namu ba. Kamar yadda muka yaki cutar Ebola, ba mu bi yadda suka suka bi ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel