Masana kimiyya sun gano maganin da ke kashe COVID-19 cikin awanni 48

Masana kimiyya sun gano maganin da ke kashe COVID-19 cikin awanni 48

Masana kimiyya a kasar Australia sun samo maganin da ke kashe kwayar cutar coronavirus a cikin sa'o'i 48.

Maganin mai suna Ivermectin ana amfani dashi ne wajen kashe kwarkwata kuma ana samun shi a fadin duniya.

Masu bincike a Jami'ar Monash sun gano cewa Ivermectin na hana rayuwar kwayar cutar SARS-CoV-2.

Amma kuma masu bincike sun gano cewa ba a gwada amfani da Ivermectin ba a kan masu cutar Coronavirus.

Kamar yadda jaridar British Tabloid Daily ta bayyana, yanzu masana kimiyya za su gano adadin kwayar maganin da dan Adam zai sha ne don tabbatarwa.

Daga karshe: Masana kimiyya gano maganin da ke kashe COVID-19 cikin awanni 48

Daga karshe: Masana kimiyya gano maganin da ke kashe COVID-19 cikin awanni 48
Source: UGC

DUBA WANNAN: Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji

Masana kimiyyar sun ce za a iya daukar a kalla wata daya cif kafin a fara gwada maganin a kan dan Adam.

"Mun gano cewa kwaya daya ta maganin na kashe duk wani digo na cutar a cikin sa'o'i 48. An samu raguwar kwayar cutar kuwa a cikin sa'o'i 24," kamar yadda Dr Kylie Wagstaff na tsangayar bincike ta Monash ya sanar a ranar Juma'a da ta gabata.

Ya kara da cewa: "A lokutan da annoba ta gallabi duniya kuma babu maganinta, samun maganin da yake akwai a sassan duniya zai iya shawo kan cutar da gaggawa. A gaskiya za a iya daukar lokaci kafin samun riga-kafin cutar."

Wannan binciken kuwa aikin tsangayar Monash ce da kuma tsangayar Peter Doherty.

An gano Ivermectin ne a 1975 kuma an fara amfani dashi a matsayin magani tun a 1981.

Yana cikin jerin magunguna masu matukar amfani da cibiyar lafiya ta duniya ta bayyana.

A kasashe masu tasowa na duniya, ana siyar da duk kwaya daya na maganin a kan $0.23. Ana iya samun shi a ko ina a duniya da sunan Stromectol ko Soolantra cream.

An fara amfani da shi ne tun a shekarun 1980 don maganin ire-iren kwayoyin cutar a jikin dan Adam, dabbobin gida da kuma na kiwo.

Ivermectin ana iya amfani da shi wajen maganin kanzuwa.

Kamfanin hada maganin da ke samar da Ivermectin mai suna MSD suna bada maganin kyauta ga kasashe masu tasowa don amfani kusan a shekaru 30 da suka shude.

Idan aka yi amfani da shi kamar yadda ya dace, kowa yana iya amfani da Ivermectin. Daga cikin illolinshi sun hada da zawo, yunkurin amai da jiri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel