A rana sai in sha kwayoyin magununa 30 - Daya daga cikin wadanda suka warke daga Coronavirus ta bayyana

A rana sai in sha kwayoyin magununa 30 - Daya daga cikin wadanda suka warke daga Coronavirus ta bayyana

Wata budurwa wacce ta samu waraka daga cutar Coronavirus a jihar Legas mai suna, Ayodeji Osowobi, ta bayyana abubuwan da ta fuskanta killace a asibiti saboda sauran alumma hadarin cutar da yadda gwamnati ke kula da wadanda suka kamu.

Ta bayyana irin magungunan da ta sha a asibiti da irin abincin da gwamnati ke basu a asibiti.

Ayodeji Osowobi ya bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita inda tace

“Na dawo Najeriya daga taron Commonwealth da na halarta a kasar Birtaniya sai na fara rashin lafiya. A matsayin mai hankali, da wuri na killace kaina.“

“Bayan yan kwanaki, sai aka ce na kamu da cutar COVID-19.“

“Wani zubin kwayoyin magani kawai nike sha. Zan sha kwayoyi 8 da safe, 13 da rana, 10 da dare.“

“Na fara kin jinin abinci da ruwa. Amma hakan nan zan tilasta kaina shan ruwa.“

“Bayan yan kwanaki, na ji jiki. Amai da gudawan na wuce tsammani.“

“Zuwa ga matasanmu, ku taimakawa kanku wajen yakar cutar nan ta hanyar kare lafiyar huhunku. Ina baku shawara ku daina shan sigari.“

“Huhu mai lafiya abune mai muhImmanci.“

KU KARANTA Yadda mutane suka yi wawaso wurin rabon tallafin kayan abinci a Kaduna

A rana sai in sha kwayoyin magununa 30 - Daya daga cikin wadana suka warke daga Coronavirus ta bayyana
Ayodeji
Asali: Twitter

Ga hotunan irin abincin da ake basu a killace

A bangare guda, Gwamnatin jihar Legas a ranar Alhamis ta sanar da kara sallamar wata mai fama da cutar Coronavirus daga asibitin jihar bayan kwashe kwanaki tana jinya.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewa an saki matar ne bayan gwaji biyu daban-daban sun nuna cewa ta barranta daga kwayar cutar.

Yace “Cikin farin cikin nike sanar muku cewa an sake sallamar mara lafiya (mace) wacce ta warke gaba daya a asibitinmu dake Yaba.“

“A yanzu mutane 32 kenan muka yi jinyarsu tare da sallamarsu a Legas.“

“Ina kyautata zaton cikin kwanaki masu zuwa zan cigaba da kawo muku labarai masu dadi“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel