An yafe wa wani gari a Sokoto kudin wutan lantarki na wata daya

An yafe wa wani gari a Sokoto kudin wutan lantarki na wata daya

- Mazauna yankin Tamaje da ke jihar Sokoto sun fada tsananin murna da annashuwa sakamakon karamcin da kamfanin wutar lantarki yayi musu

- Kamfanin samar da wutar lantarki na Kaduna (KAEDCO) ya bayyana cewa ya yafe musu kudin wutar lantarki na watan Maris gaba daya

- Kamar yadda wakilin yankin ya sanar, mazauna yankin sun yi zanga-zanga ne a ranar Litinin sakamakon halin rashin wutar lantarki da suka fada a watan Maris baki daya

Mazauna yankin Tamaje da ke jihar Sokoto sun shiga halin jin dadi da annashuwa bayan an yafe musu biyan kudin wutar lantarki na watan Maris.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, wannan ya biyo bayan taron da hukumar kamfanin wutar lantarki ta Kaduna ta yi bayan mazauna yankin sun yi zanga-zangar lumana a ranar Litinin.

An yafe wa wani gari a Sokoto kudin wutan lantarki na wata daya

An yafe wa wani gari a Sokoto kudin wutan lantarki na wata daya
Source: UGC

Mai magana da yawun masu gidajen yankin, Alhaji Saka Sadiq, yayin zantawa da manema labarai a ofishin KAEDCO na Sokoto, ya jinjinawa hukumar a kan hukuncin da ta yanke na yafe musu kudin wutan watan Maris saboda bata basu wuta ba.

Ya kara da kira gare su da su gaggauta mayar wa yankin wutar lantarki wacce suka rasa sakamakon satar wayar da barayi suka yi.

Ya ce, "Mun zanta da wakilin kamfanin wutar lantarkin kuma an tabbatar mana da cewa an mika bukatarmu Kaduna. Za a biya ta da gaggawa. A bangarenmu kuwa, Muna tabbatar da cewa mazauna yankin sun kafa rundunar masu tsaro don gadin tiransifomar bayan an saka mana."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel