Ganduje ya karawa ma'aikatan jihar Kano wa'adin cigaba da zama a gida

Ganduje ya karawa ma'aikatan jihar Kano wa'adin cigaba da zama a gida

Gwamnatin jihar Kano ta karawa ma'aikatanta hutun zama a gida na tsason wasu sati biyun domin dakile yaduwar cutar covid-19 a jihar.

Dakta Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano, ne ya sanar da hakan yayin da ya karbi rahoton kwamitin wucin gadi da ya kafa domin neman tallafin kudi. Ya ce karin wa'adin hutun yana daga cikin shawarar da gwamnatinsa ta yanke a matsayin rigakafin kare jama'a daga kamuwa da cutar covid-19 a jihar.

"Akwai fargaba har yanzu, saboda har yanzu yawan masu kamuwa da kwayar cutar da wadanda cutar ta kashe karuwa yake yi a Najeriya," a cewar Ganduje.

Bayan karbar rahoton kwamitin, gwamna Ganduje ya jinjinawa mambobin kwamitin tare da yabawa aikin da suke yi. Kazalika, ya basu tabbacin cewa nan bada dadewa ba za a raba tallafin da aka samu ga mabukata.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin kuma shugaban jami'ar Bayero ta Kano, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ya sanar da gwamnan cewa yanzu haka akwai tsabar kudi miliyan N364.6 a asusun banki.

Ganduje ya karawa ma'aikatan jihar Kano wa'adin cigaba da zama a gida
Ganduje da Farfesa Muhammad Yahuza Bello
Asali: Facebook

Sauran kayan tallafi da jama'a suka bayar ta hannun kwamitin sun hada da kayan abinci da sauran kayan amfani a gida.

Daga cikin wadanda suka bayar da tallafi mafi tsoka akwai kungiyar 'yan kasar Lebanon mazauna Kano, wadanda suka bayar da tallafin kayan abinci da darajar kudinsu ya wuce miliyan N100m.

Bayan kammala taro da mambobin kwamitin, gwamna Ganduje ya kai ziyara cibiyar killace masu dauke da cutar covid-19 da gidauniyar Dangote tare da hadin gwuiwar gwamnatin jihar Kano suka samar.

DUBA WANNAN: FG ta rabawa talakawan Kano biliyan N1.6

Cibiyar, mai jimillar gadon kwantar da marasa lafiya 509, tana da bandakuna, dakin gwaji, dakin shan magani, motar daukan marasa lafiiya, dakin ganawar ma'aikata da masana da sauransu.

Tun a ranar 29 ga watan Maris Legit.ng ta wallafa rahoton cewa hamshakin attajirin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, zai samar da wata cibiyar killace wa mai gado 600 domin duba wadanda suka kamu da kwayar cutar coronvirus a jihar Kano.

Ganduje, ne ya sanar da hakan yayin kaddamar da kwamitin neman kudin taimakawa masu karamin karfi a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel