Za mu fara gwajin maganin COVID-19 a Legas - Farfesa Abayomi

Za mu fara gwajin maganin COVID-19 a Legas - Farfesa Abayomi

- Kwamishinan Lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya ce jihar tana shirin fara yin gwajin maganin coronavirus

- Kwamishinan ya ce za a fara gwajin ne a kan wasu majinyata da ke jihar da kuma ma'aikatan hukumarsa da nufin samo tabbatacen maganin cutar

- A halin yanzu dai kasashen duniya da ke fama da cutar sun fara gudanar da gwaje-gwaje masu kama da wannan da nufin samo maganin

Kwamishinan Lafiya na jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ya ce jihar ta gama shirye-shiryen fara gwajin maganin COVID-19 a kan majiyanta a jihar tare da hadin gwiwar Cibiyar kawar da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) da wasu hukumomin.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin wata jawabi da ya yi a ranar Litinin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Za a fara gwajin maganin COVID-19 a Legas - Farfesa Abayomi
Za a fara gwajin maganin COVID-19 a Legas - Farfesa Abayomi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Labari da dumi-dumi: Tsohon malamin da ya koyar da Abacha, Dr Habibu Gwarzo ya rasu a Kano

Ya ce, "Ana gudanar da bincike masu yawa a kasashen duniya, saboda haka akwai yiwuwar nan da wani lokaci a gaba za mu samu abinda za mu iya kira takamamme maganin COVID-19. Za mu fara yin namu gwaje-gwajen a Legas tare da wasu hukumomi da NCDC kuma muna fatan sati mai zuwa za mu fara gwada magungunan a kan wasu majinyata da ma'aikatan mu a Legas.

"Muna da wurin gwajin kwayar cutar guda uku a Legas kuma muna sa ran za mu bude wasu sabbi a wasu wuraren a jihar. Guda ukun da muke da su a yanzu sun hada da Lagos State Biobank da ke asibitin Yaba, Sashin binciken kwayoyin hallita na Virus a asibitin koyarwa na jami'ar Legas da kuma Cibiyar Binciken Lafiya na kasa a Legas."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164