Karya suka shara mini, ban ce babu yunwa a Najeriya ba - Lai Mohammed ya koka kan masu yada labaran shi na bogi

Karya suka shara mini, ban ce babu yunwa a Najeriya ba - Lai Mohammed ya koka kan masu yada labaran shi na bogi

- Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya koka da yadda wasu kafofin yada labarai ke baza labaran bogi

- Ya ce masu baza labaran bogin nan na yin haka ne don janye hankalin gwamnatin tarayya a kan yakar annobar coronavirus

- Ya yi kira ga jama'ar kasar nan a kan su gujewa sauraron labaran da basu fito daga gareshi ba ko kwamitin shugaban kasar na yakar coronavirus

Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya koka da yadda labaran bogi ke yaduwa a kan gwamnatin tarayya wanda hakan ke janye hankalinsu daga yakar muguwar cutar coronavirus a kasar nan.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin, Mohammed ya jajanta cewa akwai mutanen da ke dauke hankalin mulkin shugaba Buhari daga yakar muguwar cutar coronavirus, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

A yayin da yake bada misali, ministan ya ce: "Daya daga cikin labaran bogin kwanakin nan shine wanda aka ce babu yunwa a kasar nan kuma gwamnatin tarayya ta fitar da naira biliyan dari ga 'yan Najeriya. Labarin bogi ne kuma ni ban sanar da hakan ba."

Duk da cewa ministan bai fitar da sunaye ba, amma ya ce masu yada labaran bogin basu denawa.

"Wadanda suka shirya janye hankalin gwamnatin tarayya ta hanyar yada labaran bogi, suna yin haka ne don hana yakar annobar coronavirus kuma ba za su dena ba.

KU KARANTA: Ka ajiye makamanka tun dare bai yi maka ba idan ba haka ba ka bakunci kiyama - Sakon Idriss Deby ga Shekau

"Sun yada cewa mambobin kwamitin shugaban kasar a kan yaki da coronavirus sun amince da wani salon raba duk gudumawar da ta iso. Wannan labarin bogi ne. Wadannan mutane sun shirya janye hankalin gwamnatin tarayya a kan yakar annobar coronavirus," yace.

Kamar yadda yace, dalilin da yasa gwamnatin tarayya ke jawabi kullum shine don sanar da 'yan Najeriya halin da ake ciki a kasar nan dangane da muguwar kwayar cutar.

Ya shawarci 'yan kasa da su gujewa labaran bogi tare da jaddada cewa duk labaran da basu fito daga kwamitin shugaban kasar ko ministan ba, na bogi ne.

"Dalili daya da yasa muke taron manema labarai kullum shine don sanar da 'yan kasa halin da ake ciki a kan barkewar annobar coronavirus. Duk wani labarin da bai fito daga bakin ministan ba ko kuma kwamitin shugaban kasar, kada a danganta mu da shi.

"Cibiyar yaki da yaduwar cutuka na kokarin bayani a shafinta na yanar gizo kuma za a iya samun labaran a wajensu.

"Wasu shafukan yanar gizo da aka san su da kwarewa a yada labaran bogi duk a gujesu. A dena sauraronsu," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel