Ka ajiye makamanka tun dare bai yi maka ba idan ba haka ba ka bakunci kiyama - Sakon Idriss Deby ga Shekau

Ka ajiye makamanka tun dare bai yi maka ba idan ba haka ba ka bakunci kiyama - Sakon Idriss Deby ga Shekau

- Shugaban kasar Chadi, Idris Deby ya yi kira ga shugaban 'yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau a kan ya fito daga maboyar shi ko kuma a zakulo shi

- Kamar yadda shugaban kasar ya bayyana, idan Shekau bai fito ba za su fito dashi kamar yadda suka yi wa sauran a samamen da suka kai a kwanakin nan

- A samamen da suka kai Kilkuoa da Magumeri tare da rundunar sojin kasar Chadin, sun halaka mayakan 92 tare da tasa keyar daya daga cikin manyan kwamandojin 'yan ta'addan

Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby ya yi kira ga shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, da ya fito daga maboyarshi tare da mika kanshi ko kuma a halaka shi a hakan.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da Deby ya jagoranci rundunar sojin kasar Chadi don ragargaza mayakan. Wannan samamen kuwa ya yi ajalin a kalla 'yan ta'adda 92 kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A wani jawabi da shugaban kasan yayi wa jama'ar kasar shi, ya yi magana da harshen Faransanci tare da cewa Shekau yana da damar miko kanshi ko kuma za a zakulo shi daga maboyar shi tare da kashe shi kamar yadda aka yi wa kwamandojinshi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rundunar sojin kasar Chadi ta kai wa 'yan ta'adda hari inda ta halaka mayaka 92.

Shugaban kasa Deby, wanda yace ba zai aminta da su ci galaba a kanshi ba, ya kaddamar da babban hari don daukar fansar jama'ar shi da suka kashe.

Harin mai suna Operation Wrath of Bomo an saka mishi suna ne irin na garin da aka halaka sojojin kasar Chadin kuma an fara ne a ranar Alhamis.

Hakazalika shugaban kasar ne ke jagorantar rundunar sojin don yakar 'yan ta'addan a Kelkoua da Magumeri inda suka halaka 'yan ta'addan masu yawa tare da kwashe miyagun makamai da kuma tasa keyar wani babban kwamandan rundunar 'yan ta'addan.

An zargi cewa rundunar sojin kasar Chadin ta saki wasu sojojin Najeriya wadanda mayakan ta'addancin suka yi garkuwa dasu a Magumeri, wata karamar hukuma da ke kudancin Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan basu ji da dadi ba wajen rundunar sojin Chadi sannan sun dau alkawarin kawar dasu cikin kwanaki kalilan don har kasashe masu makwabtaka suka dinga shiga.

A wani faifan bidiyo na yadda samamen ya kasance, an ga gawawwakin 'yan ta'addan tare da daruruwan makamansu wadanda wani sashensu ke rufe da jini. Sun kuma kama daya daga cikin shugabannin a yayin da yake yunkurin tserewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel