Yansanda sun kama barauniyar yara dauke da kananan yara 27 a Taraba

Yansanda sun kama barauniyar yara dauke da kananan yara 27 a Taraba

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Taraba ta sanar da kama wata mata mai suna Mary Yakubu tare da wasu kananan yara guda 27 da ta sato su daga sassa daban daban na jahar.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar, David Misal ne ya sanar da kama matar a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu, inda yace wannan ne karo na uku da suke kama matar, hakan ya kawo adadin yaran da suka ceto daga hannunta zuwa 60.

KU KARANTA: Wani mutumi ya bindige mutane 5 sakamakon sun dame shi da surutu

Yansanda sun kama barauniyar yara dauke da kananan yara 27 a Taraba

Mary Yakubu
Source: Facebook

Missal ya ce sun ceto yaran ne daga hannun Mary a ranar Lahadi a tashar Takalma dake karamar hukumar Gassol na jahar Taraba. Daga cikin yaran dake hannunta akwai mata 13 da maza 14.

Mista Misal yace tuni sun mika yara 33 da matar ta sata ga iyayensu, sa’annan sun mika sabbin yara 27 ga ma’aikatar kula da harkokin mata, yayin da suka gurfanar da matar gaban kotu.

An fara kama Mary ne a ranar 26 ga watan Feburairu a garin Bali da laifin safarar yara.

A lokacin da aka kamata na farko tana dauke da yara 23, wadanda take shirin safararsu tare da cinikinsu a wani gari, ba ta dandara ba, inda aka sake kamata a ranar 4 ga watan Maris, a wannan lokaci jagoranci Yansanda zuwa mafakarta dake Mararraban Donga inda suka ceto yara 10.

A wani labarin kuma, wani lamari mai ban takaici ya faru a jahar Bayelsa inda wasu zauna gari banza suka kwashe tarin kayan abinci da gwamnati tanadar ma jama’a a matsayin tallafi.

Kayan abincin da miyagun suka sace ya hada da buhunan shinkafa da buhunan Garri, haka zalika sun miyagun sun fasa wata ma’aijiyar kayan abinci a yankin Igbogene na garin Bayelsa, inda suka kwashe shinkafa da Garri.

Wani shaidan gani da ido da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa miyagun sun afka wurin da ake rabon abincin ne dauke da bindigu inda suka dinga harbe harbe, wanda hakan yasa jama’a tserewa, kafa mai na ci ban baki ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel