Tsohon gwamna Fayose ya bayyana abin da ya fi Coronavirus kashe yan Najeriya

Tsohon gwamna Fayose ya bayyana abin da ya fi Coronavirus kashe yan Najeriya

Tsohon gwamnan jahar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi kira ga gwamnatoci a kowanne mataki, kungiyoyin addinai, kamfanoni masu zaman kansu da kuma masu hannu da shuni da su mayar da hankali wajen tallafa ma jama’a da kayan abinci.

Daily Nigerian ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne a garin Ado Ekiti ta bakin mai magana da yawunsa, Lere Olayinka, inda ya yi kira ga wadanda abin ya shafa da su dauki shawararsa da muhimmanci.

KU KARANTA: Wani mutumi ya bindige mutane 5 sakamakon sun dame shi da surutu

Tsohon gwamna Fayose ya bayyana abin da ya fi Coronavirsu kashe yan Najeriya

Tsohon gwamna Fayose ya bayyana abin da ya fi Coronavirsu kashe yan Najeriya
Source: UGC

A cewar tsohon gwamnan, yunwa ta fi Coronavirus kashe yan Najeriya, kuma ta fi kisa cikin sauri. Ya kara da cewa za’a yi fama da matsaloli irin na tattalin arziki da ire irensu a sanadiyyar bullar Coronavirus, don haka yanzu ne ya kamata shuwagabanni su tashi tsaye su yi jagoranci.

Fayose ya jinjina ma gwamnan jahar Legas, Babajide Sanwo-Olu bisa kokarin da yake yi na kare jama’an jahar tare da dagewa da yake yi a kan shawo kan kalubalen da suka fuskantar jahar, da kuma yadda tafiyar da lamarinsa da gaskiya.

Fayose ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi koyi da gwamnatin jahar Legas wajen shayar da jama’a sabbin bayanai cikin lokaci domin rage yaduwar labaran karya da na kanzon kurege game da cutar a tsakanin al’umma.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa akwai magungunan gargajiya da ya yi amfani da su yayin da yake killace, wanda yace sun taimaka masa wajen warkewa daga cutar Coronavirus.

Kimanin mako daya kenan Gwamna Makinde ya sanar da kamuwa da cutar Coronavirus wanda hakan tasa ya killace kansa tare da kauce ma cudanya da jama’a don gudun kada ya harbe su da ita, amma bayan kwanaki 6 da aka sake gudanar da gwajin cutar a kansa, sai aka ga baya dauke da ita.

Jaridar TheCables ta ruwaito cikin wata hira da Makinde ya yi da gidan rediyon Fresh FM Ibadan ya bayyana cewa ya yi amfani da man habbatissaudah da kuma zuma, inda ake hada mai su duka sai ya sha, domin kara karfin garkuwan jikinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel