Habbatissaudah da zuma ne suka warkar da ni daga Coronavirus – Gwamna Makinde

Habbatissaudah da zuma ne suka warkar da ni daga Coronavirus – Gwamna Makinde

Gwamnan jahar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa akwai magungunan gargajiya da ya yi amfani da su yayin da yake killace, wanda yace sun taimaka masa wajen warkewa daga cutar Coronavirus.

Kimanin mako daya kenan Gwamna Makinde ya sanar da kamuwa da cutar Coronavirus wanda hakan tasa ya killace kansa tare da kauce ma cudanya da jama’a don gudun kada ya harbe su da ita, amma bayan kwanaki 6 da aka sake gudanar da gwajin cutar a kansa, sai aka ga baya dauke da ita.

KU KARANTA: Wani mutumi ya bindige mutane 5 sakamakon sun dame shi da surutu

Habbatissaudah da zuma ne suka warkar da ni daga Coronavirus – Gwamna Makinde

Habbatissaudah da zuma ne suka warkar da ni daga Coronavirus – Gwamna Makinde
Source: Facebook

Jaridar TheCables ta ruwaito cikin wata hira da Makinde ya yi da gidan rediyon Fresh FM Ibadan ya bayyana cewa ya yi amfani da man habbatissaudah da kuma zuma, inda ake hada mai su duka sai ya sha, domin kara karfin garkuwan jikinsa.

“Ni dai ga ni nan na warke, ina tabbatar muku da cewa na yi gwajin COVID-19 a ranar Alhamis, kuma a inda aka min gwajin farko aka tabbatar da cewa ina dauke da cutar, a nan aka sake min wannan gwajin, kuma sakamakon gwajin ya nuna ba na dauke da shi.

“Haka zalika a cibiyarmu ta gwaje gwaje na jami’ar Ibadan ma haka, sun sake daukan jini na don min gwaji, sakamakon wannan gwajin ma ya tabbatar bana dauke da cutar, a yanzu haka na warke sarai.

“Abokina, kuma shugaban hukumar lafiya a matakin farko na jahar Oyo, Dakta Muyideen Olatunji ne ya fada min muhimmancin habbattissaudah, musamman wajen kara karfin garkuwan jikin dan Adam, don haka sai nake hada shi da zuma, ina sha da safe da yamma.

“Da wannan nake fada ma jama’a cewa akwai magungunan gargajiya da ka iya kara musu karfin garkuwan jiki, don haka kada su wani tsorata, idan har zan iya fitar da cutar daga jikina, kowa ma zai iya.” Inji shi.

A wani labarin kuma, kafatanin ma’aikatan fadar gwamnatin jahar Kaduna na zaman dar dar biyo bayan gano wasu mutane uku a jahar Kaduna da suka kamu da cutar Coronavirus sakamakon mu’amala da suka yi da gwamnan jahar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai.

Idan za’a tuna gwamnan da kansa ya sanar da kamuwarsa da cutar, kuma tun daga wannan lokaci ya killace kansa, inda yake samun kulawa da kwararrun likitoci, sai dai jami’an kiwon lafiya sun ki amincewa su bayyana inda aka killace sauran mutane ukun.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel