Yanzu-yanzu: Mutane 6 sun sake kamuwa da cutar Coronavirus a Najeriya - NCDC

Yanzu-yanzu: Mutane 6 sun sake kamuwa da cutar Coronavirus a Najeriya - NCDC

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane shida (6) da suka kamuwa da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Litinin, 6 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An tabbatar da mutane goma(10) sun kamu da #COVID19 a Najerya, 2 a Kwara, 1 a Abuja, 2 a Edo, 1 a Rivers.“

“Kawo karfe 9:30 na yammacin 6 ga Afrilu, mutane 238 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami mutane 35 , kuma mutane 5 a rigamu gidan gaskiya.“

Lagos- 120

FCT- 48

Osun- 20

Oyo- 9

Edo- 11

Bauchi- 6

Akwa Ibom- 5

Kaduna- 5

Ogun- 4

Enugu- 2

Ekiti- 2

Rivers-2

Benue- 1

Ondo- 1

Kwara- 2

KU KARANTA: Hukumar NAFDAC ta fargar da yan Najeriya kan jabun kwayar Choloroquine daga kasar Sin

A wani labarin daban, Nahiyar Afrika na iya fuskantar kamuwar mutane 450,000 da cutar Coronavirus a watan Mayu idan ba'a harzuka wajen gwada mutane da inganta harkokin kiwon lafiya ba.

Wasu masana kimiyya daga kwalejin gyaran muhalle da likitanci dake Landan sun bayyana hakan ne bisa ga binciken lissafi da suka gudanar kan yadda adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus ta ninku cikin mako daya kacal.

Kawo yanzu mutane 9,198 suka kamu da cutar a nahiyar Afrika, 813 sun warke kuma 414 sun rigamu gidan gaskiya.

Masana Kimiyyan sun yi hasashen cewa a gabashin Afrika kadai, kowace kasa dake cikinta zasu samu akalla mutane 10,000 nan da 10 ga watan Mayu.

Kasashen da ke gabashin Afrika sune: Djibouti, Eriteria, Ethiopiya, Kenya, Madagascar, Mauritius, Ruwanda, Seysheles, Somaliya, Sudan, Tanzaniya, Uganda da Sudan ta kudu.

Yayinda cutar ta bulla a kasashe 51 cikin 56 na nahiyar, masanan sun bayyana cewa kawai matakin da za'a iya dauka domin hana wannan hasashe shine idan mutane sun daina cudanya da kuma su rika nisanta da juna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel