Hukumar NAFDAC ta fargar da yan Najeriya kan jabun kwayar Choloroquine daga kasar Sin

Hukumar NAFDAC ta fargar da yan Najeriya kan jabun kwayar Choloroquine daga kasar Sin

Hukumar tabbatar da sihhancin magunguna da abinci a Najeriya NAFDAC a ranar Litinin ta fargar da yan Najeriya kan yaduwar jabun kwayoyin maganin Chloroquine Phosphate 250mg daga kasar Sin.

A wani jawabi, Dirakta Janar na hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce kungiyar kiwon lafiyan duniya WHO ta sanar da su cewa maganin ya fara yaduwa a kasar Kamaru

Tace: "Kamfanin Jiangsu pharmceutical Inc, Astral pharmceutical New Bhupalpura, dake kasar Sin take hada jabun kwayar chloroquine phosphate 250mg ."

"Amfani da wannan kwayar ta Chloroquine phosphate 250mg na iya halaka mutum."

"Kamfanin ta Astral pharmacuticals, New Bhupalpura, China ta daura lambar karya na hukumar NAFDAC No. 0587612."

"Saboda haka ana gargadin jama'a su farga da wannan kwaya."

Hukumar NAFDAC ta fargar da yan Najeriya kan jabun kwayar Choloroquine daga kasar Sin

Hukumar NAFDAC ta fargar da yan Najeriya kan jabun kwayar Choloroquine daga kasar Sin
Source: Facebook

KU KARANTA: Yaran yan bindiga sun juya ma jagoransu baya, sun kashe shi har lahira

A bangare guda, Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane shida (6) da suka kamuwa da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Litinin, 6 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An tabbatar da mutane goma(10) sun kamu da #COVID19 a Najerya, 2 a Kwara, 1 a Abuja, 2 a Edo, 1 a Rivers.“

“Kawo karfe 9:30 na yammacin 6 ga Afrilu, mutane 238 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami mutane 35 , kuma mutane 5 a rigamu gidan gaskiya.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel