Yanzu-yanzu: An samu bullar Coronavirus na farko a jihar Kwara

Yanzu-yanzu: An samu bullar Coronavirus na farko a jihar Kwara

Kwamitin kar ta kwana na yakar COVID-19 a jihar Kwara ta tabbatar da bullar cutar na farko a jihar. Mutane biyu aka tabbatar sun kamu da cutar. TVC News ta ruwaito.

Ta farko wata matar wani mara lafiya ne da ya mutu a asibitin koyarwan jami'ar Ilori ranar Alhamis; dayan kuma wani ne da ya dawo daga kasar Birtaniya.

Gwamnatin jihar ta saki jawabin ne misalin karfe 6:33 na yammacin nan yan mintuna bayan samun sakamakon gwajin daga cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya dake Ibadan.

Gwamnatin za tayi hira da manema labarai gobe (Talata) da safe misalin karfe 11 na safe domin cikakken bayanai kan matakan da ake dauka wajen dakile cutar.

DUBA WANNAN: Da duminsa: An sake sallamar mutane biyu bayan sun warke daga cutar Coronavirus

Yanzu-yanzu: An samu bullar Coronavirus na farko a jihar Kwara

Yanzu-yanzu: An samu bullar Coronavirus na farko a jihar Kwara
Source: Twitter

A jihar Kaduna kuwa, kafatanin ma’aikatan fadar gwamnatin jahar na zaman dar dar biyo bayan gano wasu mutane uku a jahar Kaduna da suka kamu da cutar Coronavirus sakamakon mu’amala da suka yi da gwamnan jahar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai.

Jaridar Guardian ta ruwaito ma’aikatan fadar gwamnatin jahar, gidan Sir Kashim Ibrahim na cikin zulumi saboda rashin sanin matsayinsu, musamman ga wadanda suka mu’amalanci gwamnan sosai da sosai.

Gwamnatin jihar ta ce kawo yanzu an tura sanfurin jinin mutane 89 Abuja domin gwaji.

Kwamishanar kiwon lafiyan jihar, Dakta Amina Mohammed Baloni, wacce ta bayyana hakan ranar Litinin ta ce cikin samfura 89 da aka tura, sakamakon ya nuna 5 sun kamu, 77 basu kamu ba, kuma ana sauraron 8.

Baloni a jawabin da ta saki ranar Litinin ta ce kawo yanzu an katabta sunayen mutane 119 da ake nema.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel