Rabawa talakawa shinkafa, daukan ma'aikata 774,000 da sauran matakan rage radadi 7 da FG ta dauka

Rabawa talakawa shinkafa, daukan ma'aikata 774,000 da sauran matakan rage radadi 7 da FG ta dauka

Zainab Ahmed, ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta sanar da kunshin matakan da gwamnatin tarayya (FG) ta dauka domin rage radadin kuncin rayuwa da annobar covid-19 ta haifar.

Da take magana da manema labarai ranar Litinin a Abuja, ministar ta ce sabbin matakan ba zasu hana sauran matakan ragewa jama'a zafi da babban bankin kasa (CBN) da ma'aikatar jin dadi da walwala suka sanar ba.

Ga matakai 9 da ministar ta bayyana cewa FG ta dauka:

1. Daukan 'yan Najeriya 774,000 aiki

Ministar ta bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin a dauki 'yan Najeriya 774,000 (kimanin mutum 1000 kowacce karamar hukuma) aiki na hidimtawa jama'a a karkashin kulawar hukumar samar da aiyuka (NDE)

A cewarta, FG ta ware biliyan N60 daga tallafin da ta samu na yaki da annobar covid-19 domin biyan ma'aikatan da za dauka.

2. Hukumar kwastam za ta raba duk shinkafar da ta kama

Domin tabbatar da ganin cewa ba a shiga matsalar abinci a kasa ba, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarni rabawa 'yan Najeriya dukkan shinkafar da ke cikin manyan motocin dako 150 da ake tsare da su.

3. Kokarin samar wa da cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) $82m

A cewar ministar, cibiyar NCDC za ta iya cin moriyar kudin da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan $90 a karkashin wani tsari mai taken REDISSE (regional disease surveillance system).

Zainab ta bayyana cewa tuni NCDC ta ci moriyar $8m daga cikin kudin, yanzu kuma FG ta aika bukatar neman samun sauran dala miliyan $82 da suka rage.

Rabawa talakawa shinkafa, daukan ma'aikata 774,000 da sauran matakan rage radadi 7 da FG ta dauka
Zainab Ahmed
Asali: UGC

4. Neman $6.9bn daga IMF, bankin duniya da AfDB

Ministar ta bayyana cewa FG ta aika bukatar neman rancen dalar Amurka biliyan $6.9 daga hukumar lamunin kudi ta kasa da kasa (IMF), bankin duniya, da bankin raya nahiyar Afrika (AfDB).

Ta bayyana cewa za a bawa Najeriya rancen kudin ne a karkashin tsarin bawa kasashe rancen gata da babu sharuda masu tsauri domin su yaki annobar cutar covid-19.

5. Karawa ma'aikatan lafiya na tarayya alawus

"Za a inganta alawus din da ake bawa ma'aikatan lafiya saboda hatsarin aikin da ke ciki aikinsu. Gwamnatin tarayya na yin kira ga jihohi da su kwaiwayi wannan sabon tsari," a cewar ministar.

DUBA WANNAN: Coronavirus: Hotunan cibiyar killacewa da gidauniyar Dangote ta gina a Kano

6. Ware biliyan N500 don gyaran asibitoci

Za a yi amfani da kudin ne wajen inganta aiyukan wasu asibitoci a fadin bisa shawarar kwamitin da shugaba Buhari ya kafa a kan annobar covid-19.

7. Dakatar da biyan bashin da FG ke bin jihohi da basukan da CBN ta bayar

Bisa la'akari da raguwar kudin shiga da FG ke fuskanta, lamarin da a nan gaba za shafi kason da take bawa jihohi, shugaba Buhari ya umarci ma'aikatar kudi ta tuntubi CBN domin sake duba sharudan biyan basuka.

8. Yin sassauci ga kamfanoni da masu saka hannun jari a tattalin arziki

Da take amsa tambaya a kan shirin FG a kan masu kanana da matsaikatan masana'antu, Zainab ta bayyana dokar harkokin kasuwanci ta shekarar 2020 ba bayar da damar daukewa masu irin wadannan kananan masana'antu biyan haraji.

9. Rage burikan da gwamnati ta saka a cikin kasafin kudin 2020

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel