Coronavirus: Mutane 119 da muke nema yanzu - Gwamnatin jihar Kaduna

Coronavirus: Mutane 119 da muke nema yanzu - Gwamnatin jihar Kaduna

Yayinda jihar Kaduna ta samu karin mai cutar Coronavirus daya ranar Lahadi, wanda ya kai adadin masu cutar a jihar 5, gwamnatin jihar ta ce kawo yanzu an tura sanfurin jinin mutane 89 Abuja domin gwaji.

Kwamishanar kiwon lafiyan jihar, Dakta Amina Mohammed Baloni, wacce ta bayyana hakan ranar Litinin ta ce cikin samfura 89 da aka tura, sakamakon ya nuna 5 sun kamu, 77 basu kamu ba, kuma ana sauraron 8.

Baloni a jawabin da ta saki ranar Litinin ta ce kawo yanzu an katabta sunayen mutane 119 da ake nema.

Tace: "Gwamnatin jihar na dauka tsauraran matakai wajen dakile yaduwar cutar COVID-19 tun watan Febrairu ta hanyar tuntubar shugabannin asibitocin jihar kan yadda za'a shawo kan lamarin."

"Mun karfafa cibiyar takaita yaduwar cututtukan (dake jihar) ta hanyar tura kwararrun ma'aikata wajen masu kula da marasa lafiya yanzu."

"Bugu da kari, ma'aikatar ta kammala shirin samar da gidan killace mutane mai dakuna 69 domin ajiye wadanda cutan ya fara bayyana jikinsu."

"Ana kyautata zaton za'a bude wajen wannan makon."

"Hakazalika, gwamnatin jihar Kaduna ta kammala shirin kafa dakin binciken gwaji tare da hadin kan asibitin koyarwan jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya, domin gwajin mutane."

Coronavirus: Mutane 119 da muke nema yanzu - Gwamnatin jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta fara biyan N20,000 ga wasu talakawa 84,000 da suka fito daga kananan hukumomin jihar Kano 15

A bangare guda, Nahiyar Afrika na iya fuskantar kamuwar mutane 450,000 da cutar Coronavirus a watan Mayu idan ba'a harzuka wajen gwada mutane da inganta harkokin kiwon lafiya ba.

Wasu masana kimiyya daga kwalejin gyaran muhalle da likitanci dake Landan sun bayyana hakan ne bisa ga binciken lissafi da suka gudanar kan yadda adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus ta ninku cikin mako daya kacal.

Kawo yanzu mutane 9,198 suka kamu da cutar a nahiyar Afrika, 813 sun warke kuma 414 sun rigamu gidan gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel