Buratai ya ce sun daina fallasa shirye shiryen da suka tanadar ma Boko Haram

Buratai ya ce sun daina fallasa shirye shiryen da suka tanadar ma Boko Haram

Babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa sun daina bayyana irin shirin da suka tanadar ma kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, don haka zai kasance sirri ne.

Daily Trust ta ruwaito Buratai ya bayyana haka ne a yayin taron cin abincin dare da rundunar ta shirya don karrama tsohon kwamandan yaki da Boko Haram na Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Olusegun Adeniyi a garin Borno.

KU KARANTA: Tashin hankali: Mutane 3 da suka kamu da Coronavirus a Kaduna sun yi mu’amala da El-Rufai

Buratai ya ce sun daina fallasa shirye shiryen da suka tanadar ma Boko Haram

Buratai ya ce sun daina fallasa shirye shiryen da suka tanadar ma Boko Haram
Source: Facebook

Buratai ya bayyana cewa rundunar ba za ta sake fallasa shirinta ba, amma ya yi kira ga dakarun rundunar Sojin kasa da su kasance cikin shiri domin kuwa akwai aiki na musamman da za su gudanar nan bada jimawa ba.

“Ba za mu fadi shirye shiryen mu ba, amma na san da zarar kun fara natsuwa a aikin, babban aiki zai same ku, kuma dukkanin sabbin kwamandojin su shirya akwai aiki a gabansu.” Inji Buratai ga sabon kwamandan Manjo Janar Farouk Yahaya.

Buratai ya jinjina ma tsohon kwamanda Adeniyi bisa jarumat da kuma salon shugabancinsa, inda ya ce: “Wannan karramawar ta yi daidai ga duk mutumin da ya nuna kwarewa, jajircewa da fahimtar yanayin yakin da ake yi.

“Ya zo ne a daidai lokacin da yan ta’adda ke yawan kai farmaki a sansanin Sojoji, amma daga zuwansa ya dakatar da wannan.” Inji shi. Sa’annan yace dauke da kwamandan yaki daga faggen ba wani sabon abu bane a aikin Soja.

A nasa jawabin, sabon kwamandan, Manjo Janar Faruk Yahaya ya tabbatar ma Buratai cewa zai yi iyakan kokarinsa don ganin sun cimma manufar da ak sanya a gaba.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Borno ta sanar da fara aikin sabunta gidaje 500 da kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka lalata a garin Kawuri na karamar hukumar Konduga na jahar Borno.

A jawabinsa, Gwamna Zulum ya bayyana cewa gwamnati ta kammala gina gidaje 250 daga cikin 500 da ta kuduri aniyar sabuntawa, sa’annan ya kara da cewa kammala gidajen zai baiwa yan gudun hijira damar komawa matsuguninsu.

Don haka gwamnan ya nemi dan kwangilar ya gaggauta kammala aikin sabunta gidajen zuwa ranar 15 ga watan Yuni kamar yadda aka shiga yarjejeniya da shi, kuma ya amince, domin baiwa yan gudun hijira daman cigaba da walwala.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel