Yan bindiga sun yi sama da fadi kayan tallafin da gwamnati ta tanadar ma jama’a

Yan bindiga sun yi sama da fadi kayan tallafin da gwamnati ta tanadar ma jama’a

Makiyinka na tare da kai, kamar yadda masu iya magana ke yawan fadi, hakan ya yi daidai da abin da ya faru a jahar Bayelsa inda wasu zauna gari banza suka kwashe tarin kayan abinci da gwamnati tanadar ma jama’a a matsayin tallafi.

Jaridar The Nation ta ruwaito kayan abincin da miyagun suka sace ya hada da buhunan shinkafa da buhunan Garri, haka zalika sun miyagun sun fasa wata ma’aijiyar kayan abinci a yankin Igbogene na garin Bayelsa, inda suka kwashe shinkafa da Garri.

KU KARANTA: Tashin hankali: Mutane 3 da suka kamu da Coronavirus a Kaduna sun yi mu’amala da El-Rufai

Yan bindiga sun yi sama da fadi kayan tallafin da gwamnati ta tanadar ma jama’a

Gwamnan Bayelsa
Source: UGC

Wani shaidan gani da ido da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa miyagun sun afka wurin da ake rabon abincin ne dauke da bindigu inda suka dinga harbe harbe, wanda hakan yasa jama’a tserewa, kafa mai na ci ban baki ba.

Nan da nan bayan kowa ya tsere an bar musu wurin ne suka kwashi iya abin da zasu iya diba, suka kuma fice zuwa cikin wani daji, daga bisani masu rabon sun tabbatar da abincin da yan bindigan suka kwashe na karamar hukumar Sagbama, Ekeremor, da kudancin Ijawa ne.

A yan kwanakin nan ne gwamnatin jahar Bayelsa ta sanar da shirinta na tallafa ma gajiyayyu domin rage musu radadin dokar hana zirga zirga da gwamnatin ta kakaba musu sakamakon yaduwar cutar Coronavirus.

Haka zalika gwamnan jahar, Douye Diri ya rattafa hannu kan dokar garkame dukkanin kasuwannin jahar tare da hana zirga zirga don kare yaduwar cutar, duk kuwa da cewa bata bulla a jahar ba.

A wani labarin kuma, wasu rahotanni sun tabbatar da mutuwar wani kasurgumin dan bindiga mai garkuwa da mutane a jahar Katsina mai suna Abdulhadi Dan Nashe, kamar yadda jaridar Katsina Post ta ruwaito.

Majiyar ta kara da cewa dalilin wannan rashin fahimta da ya kunno kai a tsakanin yan bindigan baya rasa nasaba da wata tirka tirka da ta taso tsakanin Dan Nashe da matarsa, wanda ita kan kanwa ce ga wani shugaban yan bindiga, mai suna Dangote.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu yan bindiga dake biyayya ga Dangote ne suka kai samame gidan Dan Nashe, inda suka kashe shi har lahira. Shi dai Dan Nashe ya yi kaurin suna wajen satar mutane, shirya hare hare da kuma ciniki da fataucin miyagun makamai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel