FG ta rabawa talakawan Kano biliyan N1.6

FG ta rabawa talakawan Kano biliyan N1.6

Gwamnatin tarayya ta fara biyan N20,000 ga wasu talakawa 84,000 da suka fito daga kananan hukumomin jihar Kano 15.

Shugabar shirin bayar da tallafi a karkashin ma'aikatar jin kai da walwalar jama'a, Dakta Temitope Sinkaiye, ta sanar da hakan yayin wata ziyarar ban girma da suka kai ofishin mataimakin gwamnan jihar Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna.

A cewarta, rabon tallafin kudin na daga cikin shiri da manufar gwamnatin tarayya na inganta rayuwar talakawa da masu karamin karfi a fadin kasa.

Ta bayyana cewa ana bawa talakawan N20,000 kowanne wata a matsayin alawus da zai basu damar fara kananan sana'o'i da za su basu damar taimakon kansu da iyalansu, kamar yadda shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarni.

FG ta rabawa talakawan Kano biliyan N1.6
Rabon tallafin kudi ga talakawa a Abuja
Asali: Twitter

Kazalika, ta bayyana cewa an gudanar da bita ga wadanda suka ci moriyar tallafin domin ilimantar da su a kan yadda za su iya tsimi da ajiya domin samun jarin fara kananan sana'o'i.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin tarayya (FG) ta sanar da cewa ta karbi rukunin farko na kayan duba lafiya da ta sayo daga kasar Turkiyya domin dakilewa yaduwar annobar coronavirus tare da duba lafiyar wadanda suka kamu da cutar.

DUBA WANNAN: Daya daga cikin gwamnonin Najeriya 5 da suka kamu da cutar covid-19 ya warke

Wani jirgin sama ne, Boeing 777, mai lamba 5N-BWI, ya sauke kayan a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da daren ranar Asabar bayan ya kwaso su daga Istanbul ta kasar Turkiyya.

Jirgin ya tashi ne daga Najeriya da safiyar ranar Asabar, sannan ya dawo Najeriya a ranar tare da kayan da ya dauko daga kasar Turkiyya mai nisan tafiyar sa'o'i 7 daga Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jirgin zai sake tashi zuwa kasar China a ranar Litinin domin sake dauko wani rukuni na kayan aikin duba lafiyar jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: