Hukuma za ta hukunta Kyle Walker bayan ya saba dokar haramta shiga Jama'a

Hukuma za ta hukunta Kyle Walker bayan ya saba dokar haramta shiga Jama'a

A halin yanzu kun ji yadda Coronavirus ta ke hallaka daruruwan Bayin Allah a Birtaniya. Duk da haka akwai wadanda su ke yi wa matakan da aka sa kunnen kashi a kasar Ingila.

‘Dan wasan kwallon kafa, Kyle Walker ya yi watsi da umarnin da aka bada na hana fita cikin jama’a da kuma shiga cincirindo, inda ya kira wasu mata su ka cashe har gidansa.

Rahotanni daga Jaridar Mirror sun bayyana cewa ‘Dan wasan ya kira wasu Mata biyu masu zaman kansu zuwa gidansa, inda su ka shafe kimanin sa’a uku su na shanawa a cikin daki.

Kyle Walker wanda ya ke bugawa kungiyar Manchester City kwallo ya yi wannan abu ne a ranar da aka ji ya na bada shawara ga jama’a su zauna a gidajensu ba tare da sun fita ko ina ba.

Yanzu dai ‘Dan wasan bayan ya fito ya na bada hakuri game da ba dai-dan da ya yi ba. Akwai yiwuwar a ci shi tarar makudan kudi a dalilin bijirewa umarnin hukumomin da ya yi.

KU KARANTA: COVID-19 ta kashe tsohon Shugaban Libiya a gadon asibiti

Hukuma za ta hukunta Kyle Walker bayan ya saba dokar haramta shiga Jama'a
Za a hukunta Kyle Walker saboda karya doka a kasar Ingila
Asali: Getty Images

A farkon shekarar nan ne Walker ya rabu da Budurwarsa da su ka dade tare watau Annie Kilner. Kilner ta rabu da Tauraron ne bayan ta ji labarin ya dirkawa Lauryn Goodman ciki.

Babu mamaki kadaicin gwauranta da kuma zaman kullen da annobar Coronavirus ta jefa jama’a ne ya sa Kyle Walker ya sa a kawo masa wadannan ‘Yan mata gida domin debe kewa.

Walker ya tare ne da wata Yarinya ‘Yar shekara 21 mai suna Louise McNamara da kuma wata Budurwa daga kasar Brazil a katafaren gidansa da ke Unguwar Hale a Garin Cheshire.

Louise McNamara wanda ta ke karatun Digiri a wata Jami’a da ke Garin Manchester ta bayyana cewa wani Mai gidanta ne gayacce ta zuwa gidan Tauraron ‘Dan wasa Kyle Walker.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel