Gwamnatin Borno ta sake gina gidaje 500 da mayakan Boko Haram suka lalata

Gwamnatin Borno ta sake gina gidaje 500 da mayakan Boko Haram suka lalata

Gwamnatin jahar Borno ta sanar da fara aikin sabunta gidaje 500 da kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka lalata a garin Kawuri na karamar hukumar Konduga na jahar Borno.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ne ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki da ya kai Konduga a ranar Lahadi, 5 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Alhaki dan kwikwiyo: Yaran yan bindiga sun juya ma jagoransu baya, sun kashe shi har lahira

Gwamnatin Borno ta sake gina gidaje 500 da mayakan Boko Haram suka lalata

Gwamnatin Borno ta sake gina gidaje 500 da mayakan Boko Haram suka lalata
Source: UGC

A jawabinsa, Gwamna Zulum ya bayyana cewa gwamnati ta kammala gina gidaje 250 daga cikin 500 da ta kuduri aniyar sabuntawa, sa’annan ya kara da cewa kammala gidajen zai baiwa yan gudun hijira damar komawa matsuguninsu.

Don haka gwamnan ya nemi dan kwangilar ya gaggauta kammala aikin sabunta gidajen zuwa ranar 15 ga watan Yuni kamar yadda aka shiga yarjejeniya da shi, kuma ya amince, domin baiwa yan gudun hijira daman cigaba da walwala.

“Idan muka samu nasarar sake tsugunar da jama’an Kawuri a gidajensu, daga nan za mu wuce Umarari, muna fata jama’anmu su yi noman bana a watan Yuni.” Inji shi.

Sa’annan gwamnan ya nemi kwamandan rundunar Soji na wannan yanki ya tabbatar da tsaron rayukan jama’an yankin tare da dukiyoyinsu, domin ganin cewa ba’a sace kayan aikin gine ginen ba.

Daga karshe gwamnan ya baiwa matasan sa kai, da kungiyar mafarauta karin motocin sintiri domin taimaka musu a aikin da suke yin a tabbatar da tsaro a yankin.

A wani labarin kuma, wasu rahotanni sun tabbatar da mutuwar wani kasurgumin dan bindiga mai garkuwa da mutane a jahar Katsina mai suna Abdulhadi Dan Nashe, kamar yadda jaridar Katsina Post ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa Dan Nashe ya gamu da ajalinsa ne a hannun yaransa bayan sun yi masa bore, sun juya masa baya sakamakon wata rashin fahimta da aka samu a tsakaninsu.

Majiyar ta kara da cewa dalilin wannan rashin fahimta da ya kunno kai a tsakanin yan bindigan baya rasa nasaba da wata tirka tirka da ta taso tsakanin Dan Nashe da matarsa, wanda ita kan kanwa ce ga wani shugaban yan bindiga, mai suna Dangote.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel