Alhaki dan kwikwiyo: Yaran yan bindiga sun juya ma jagoransu baya, sun kashe shi har lahira

Alhaki dan kwikwiyo: Yaran yan bindiga sun juya ma jagoransu baya, sun kashe shi har lahira

Wasu rahotanni sun tabbatar da mutuwar wani kasurgumin dan bindiga mai garkuwa da mutane a jahar Katsina mai suna Abdulhadi Dan Nashe, kamar yadda jaridar Katsina Post ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa Dan Nashe ya gamu da ajalinsa ne a hannun yaransa bayan sun yi masa bore, sun juya masa baya sakamakon wata rashin fahimta da aka samu a tsakaninsu.

KU KARANTA: Buhari ya gargadi Sojoji da su kauce ma cin zarafin yan Najeriya saboda dokar ta-baci

Majiyar ta kara da cewa dalilin wannan rashin fahimta da ya kunno kai a tsakanin yan bindigan baya rasa nasaba da wata tirka tirka da ta taso tsakanin Dan Nashe da matarsa, wanda ita kan kanwa ce ga wani shugaban yan bindiga, mai suna Dangote.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu yan bindiga dake biyayya ga Dangote ne suka kai samame gidan Dan Nashe, inda suka kashe shi har lahira. Shi dai Dan Nashe ya yi kaurin suna wajen satar mutane, shirya hare hare da kuma ciniki da fataucin miyagun makamai.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Katsina a karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari ta umarci kafatanin ma’aikatan gwamnati da su koma bakin aikinsu daga ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu.

Legit.ng ta ruwaito gwamnatin ta sanar da haka ne cikin wata wasika dake dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jahar, Alhaji Idris Usman Tune dauke da kwanan watan 5/04/2020.

Sanarwar ta bayyana cewa: “Biyo bayan matakin da gwamnatin jahar Katsina ta dauka na umartar ma’aikatun gwamnatin jaha da na kananan hukumomi su zauna a gida domin kiyaye yaduwar cutar COVID-19, amma a yanzu bayan gudanar da nazari tare da duba shawarar masana, Gwamna Aminu Bello Masari ya umarci ma’aikatan gwamnati su koma bakin aiki daga ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu, 2020.

“Ma’aikatan za su gudanar da ayyukan da ba’a rasa ba daga karfe 10 na safe zuwa karfe 2 na rana, za’a cigaba da haka tsawon mako daya cur. Amma dukkanin makarantun gaba da sakandari, na sakandari na kudi da na gwamnati za su cigaba da zama a kulle har sai yadda hali ya yi.

“Haka zalika ana kira ga ma’aikata da su kasance suna dabbaka ka’idar kauce ma shiga cunkoson jama’a, tsayawa nesa nesa da juna, wanke hannuwa da kuma amfani da sinadarin Sanitizer don tabbatar da an kare bullar COVID-19 a Katsina.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel