An sallami mutumin farko da ya kamu da Coronavirus a jihar Osun tare da mutane 109

An sallami mutumin farko da ya kamu da Coronavirus a jihar Osun tare da mutane 109

Gwamnatin jihar Osun ta sallami mutumin farko da ya kamu da cutar Coronavirus tare da mutane 109 da suka shiga jihar daga kasar Birtaniya da Cote d’Ivoire, bayan an tabbatar basu dauke da cutar.

Gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai a gidan gwamnatin jihar dake Abere, Osogbo.

Gwamna Oyetola yace: "Daya daga cikin mutanen farko da ya kamu da cutar a Osun ya samu waraka kamar yadda gwaji biyu daban-daban suka nuna bisa ga sharrudan cibiyar NCDC."

"Hakazalika an saki Mutane 109 da aka yiwa gwaji bayan sakamakon gwajinsu ya nuna cewa basu kamu ba."

"Daga cikin 11 sun wuce jihar Oyo, 2 sun nufi Legas, 1 Ogun, 3 jihar Edo, 3 jihar Abiya, 4 jihar Delta, 1 jihar Imo, sauran 85 kuma zasu cigaba da zama a Osun."

"An basu shawara su cigaba da kula da kansu kuma su kira layukan bukatar gaggawa idan suka fara jin wani rashin lafiya."

An sallami mutumin farko da ya kamu da Coronavirus a jihar Osun tare da mutane 109

Oyetola
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Mutane 5 sun sake samun waraka daga Coronavirus, an sallamesu

Idan ba a manta ba, kwanan nan mu gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya fadada kwamitin yaki da COVID-19 a jihar Sokoto domin hana wannan cuta yaduwa a cikin jihar.

Domin hana yaduwar cutar COVID-19, a jihar Sokoto, gwamnati ta bayyana cewa za ta fara yawo daga gida zuwa gida domin binciken wadanda su ka yi tafiya kwanan nan.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Hum Angle, gwamnatin jihar Sokoto za ta rika binciken wadanda su ka ziyarci kasashen ketare inda da wannan cuta ta yi kamari.

Haka zalika gwamnatin jihar ta bakin Ma’aikatar kiwon lafiya ta ce, za ta sa ido ga Bayin Allah da su ka kai ziyara zuwa jihohin Najeriya da cutar ta Coronavirus ta shiga.

Mai girma Kwamishinan lafiyan, Muhammad Ali Inname, ya bayyana cewa duk da babu wanda ya kamu da wannan cuta a jihar, su na daukar matakan kare Bayin Allah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel