Da duminsa: Mutane 5 sun sake samun waraka daga Coronavirus, an sallamesu

Da duminsa: Mutane 5 sun sake samun waraka daga Coronavirus, an sallamesu

Gwamnatin jihar Legas a ranar Lahadi ta sanar da cewa an sake sallamar mutane biyar masu cutar Coronavirus bayan samun waraka a asibitin jinyar cututtuka dake unguwar Yaban jihar.

Gwamnan jihar Legas da kansa, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita da yammacin Lahadi, 5 ga watan Afrilu, 2020.

Yace: "Ya ku al'ummar jihar Legas, a jiya (Asabar) na sanar muku cewa mun sallami mutum daya daga asibitin jinyar cututtuka dake Yaba. A yau Ina farin cikin sanar muku cewa mutane biyar (maza biyu da mata uku) cikin akwai wani dan shekara 10 da haihuwa sun samu waraka daga cutar #COVID19."

"Tuni a mayar da wadannan mutane biyar wajen iyalansu. Yanzu jimillan mutane 29 suka samu waraka tare da sallama a asibitinmu dake Yaba."

"Duk da cewan akwai alamun nasara kan cutar COVID-19, ya kamata mu zange dantse wajen takaita yaduwarta."

Da dauminsa: Mutane 5 sun sake samun waraka daga Coronavirus, an sallamesu

Da dauminsa: Mutane 5 sun sake samun waraka daga Coronavirus, an sallamesu
Source: UGC

Gwamnatin jihar Osun ta sallami mutumin farko da ya kamu da cutar Coronavirus tare da mutane 109 da suka shiga jihar daga kasar Birtaniya da Cote d’Ivoire, bayan an tabbatar basu dauke da cutar.

Gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai a gidan gwamnatin jihar dake Abere, Osogbo inda yace: "Daya daga cikin mutanen farko da ya kamu da cutar a Osun ya samu waraka kamar yadda gwaji biyu daban-daban suka nuna bisa ga sharrudan cibiyar NCDC."

"Hakazalika an saki Mutane 109 da aka yiwa gwaji bayan sakamakon gwajinsu ya nuna cewa basu kamu ba."

A bangare guda, Gwamnatin jahar Lagas ta sanar da cewar wani mutum dan shekara 36 ya mutu sakamakon Coronavirus a jahar.

Kwamishinan lafiya na jahar Lagas, Farfesa Akin Abayomi, ya bayar da sanarwar ya shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 5 ya watan Afrilu.

Ya bayyana cewa dan Najeriyan ya mutu a ranar Asabar a wata cibiyar lafiya mai zaman kanta.

Abayomi ya tabbatar da mutuwar a matsayin na biyu da faru sanadiyar Coronavirus a Lagas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel