Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa

Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa

A makon jiya ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa sojojin kasar Chadi sun kai wa wani mummunan harin daukan fansa a kan mayakan kungiyar Boko Haram da suka fara kai wa dakarun sojojin kasar ta Chadi harin kwanton bauna.

Sojojin kasar Chadi, bisa umarnin shugaban kasarsu, Idris Derby, sun kashe dumbin mayakan kungiyar Boko Haram bayan sun yi wata doguwar musayar wuta a tsakaninsu.

Ganin irin barnar da dakarun sojojin suka yi wa mayakansa, shugaban tsohuwar kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabon sakon sautin murya domin karafa gwuiwar mayakansa tare da yin gargadi na musamman ga shugaba Derby.

A cikin wani takaitaccen sautin murya cikin harshen Hausa da jaridar Sahareporters ta wallafa a shafinta na tuwita, za a iya jin muryar Shekau yana magana cikin sanyin murya, yana cewa, "mutanen Chadi ku tashi, wannan zaman da kuke yi a kasarku ba na Qur'ani bane, ba na hadisin Annabi ne, ba alkalancin annabi Muhamadu bane ake yi, don wannan muka tashi aiki, idan a hakan kuna ganin za ku iya yi, to fa Allah mai taimako ne, kuma Allah ya fi karfin kowa, Allah ya taimaka mana."

A karshen faifan sautin muryar, Shekau ya yi magana cikin harshen larabci tare da ambaton sunan shugaban kasar Chadi, Idriss Derby.

Saurari sautin muryar:

Ko a ranar 2 ga watan Afrilu, Legit.ng ta wallafa rahoton cewa jiragen yaki na rundunar sojin sama ta Najeriya a karkashin atisayen 'Operation Lafiya Dole' sun yi luguden wuta tare da baje daya daga cikin manyan mafakar mayakan kungiyar Boko Haram da ke Parisu a cikin dajin Sambisa.

Luguden wutar ya yi sanadiyar mutuwar dumbin mayakan kungiyar Boko Haram tare da lalata dukkan sansanin.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace mai bawa gwamna Sule shawara, an kama daya daga cikinsu

A cikin jawabin da darektan yada labaran atisayen rundunar soji, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya fitar ya ce rundunar soji za ta cigaba da rike wuta a yakin da take yi da 'yan ta'adda.

"Daya daga cikin manyan hare-hare na kwanan baya bayan nan da rundunar soji ta kai a kan 'yan Boko Haram, shine na maboyarsu da ke Parisu a cikin dajin Sambisa a ranar 31 ga watan Maris. Na'urorin cikin jirgi yaki masu ido sun hango maboyar 'yan Boko Haram da motsinsu a wurin.

"Jiragen yaki sun yi luguden wuta a sansanin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dumbin mayakan Boko Haram tare da baje mafakar tasu," a cewar jawabin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel