Saba dokar hana fita: Jami'an tsaro sun damke motoci 51, babura 46 a Abuja

Saba dokar hana fita: Jami'an tsaro sun damke motoci 51, babura 46 a Abuja

Jami'an tsaron tabbatar da dokar hana fita a birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin kwamishanan yan sandan FCT, Bala Ciroma, sun damke motoci 51, babura 46 da keken adaidata sahu 9, sakamakon saba doka.

Jami'an tsaron sun kwace wadannan ababen hawan ne daga hannun mammalakansu yayinda suka fito waje maimakon zamansu a gida kamar yadda shugaban kasa yayi umurni.

Kakakin hukumar yan sandan Abuja, DSP Anjuguri Manzah, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Asabar.

Ciroma ya ce an kama motoci, babura da kekunan adaidaita sahun ne a unguwannin Nyanya, Dutse Alhaji, Karu, Jabi, Kado, Life-camp, Mpape, Zuba, dss.

Ya ce ababen hawan zasu kasance hannun hukuma har sai wa'adin kwanaki 14 na dokar da gwamnatin tarayya ta sa ya shude.

KU KARANTA: Ba Ma’aikacinmu ba ne ya ke dauke da kwayar cutar COVID-19 – Inji NNPC

Hakazalika kwamishanan yan sandan Abuja ya yi kira da al'umma su kasance masu bin doka a yunkurin da gwamnati ke yi hana yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya.

Yace: "Bugu da kari, muna kira ga mazauna birnin tarayya su bi dokar kwamitin kar ta kwana yaki da COVID-19, wacce ta ce an amince mutane su sayar da kayan abinci daga karfe 10 zuwa 2."

"Saboda haka, ana bukatan dukkan mazauna Abuja su kasance cikin gidajensu ranar Lahadi, saboda za'a damke duk wanda ya saba doka."

Saba dokar hana fita: Jami'an tsaro sun damke motoci 51, babura 46 a Abuja
Hoton motoci (Ba wadanda aka kwace ba)
Asali: Depositphotos

A bangare guda, Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane goma (10) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Lahadi, 5 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An tabbatar da mutane goma(10) sun kamu da #COVID19 a Najerya, 8 a Legas, 2 a Abuja, 2 a Edo.“

“Kawo karfe 1:15 na ranar 5 ga Afrilu, mutane 224 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami mutane 27 , kuma mutane 5 a rigamu gidan gaskiya.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel