Yanzu-yanzu: An samu karin mutane 5 sun kamu da cutar Coronavirus, jimilla 214

Yanzu-yanzu: An samu karin mutane 5 sun kamu da cutar Coronavirus, jimilla 214

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane biyar(5) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Asabar, 4 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An tabbatar da mutane ashirin (20) sun kamu da #COVID19 a Najerya, 3 a Bauchi, 2 a Abuja.“

“Kawo karfe 10:11 na daren 4 ga Afrilu, mutane 214 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami mutane 25 , kuma mutane 4 a rigamu gidan gaskiya.“

Jihar Lagos- 109

Birnin tarayya Abuja - 43

Jihar Osun- 20

Jihar Oyo- 9

Jihar Akwa Ibom- 5

Jihar Ogun- 4

Jihar Edo- 7

Jihar Kaduna- 4

Jihar Bauchi- 6

Jihar Enugu- 2

Jihar Ekiti- 2

Jihar Rivers-1

Jihar Benue- 1

Jihar Ondo- 1

Yanzu-yanzu: An samu karin mutane 5 sun kamu da cutar Coronavirus, jimilla 214
jimilla 214
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mutum daya ya sake warkewa daga Coronavirus, an sallameshi

Wannan ya biyo bayan sake waiwayen da gwamnatin jihar Bauchi tayi kan wata sanarwa da ta fitar na sanya dokar ta baci da zata rufe jihar na tsawon kwanaki 14 domin dakile shiga da yaduwar cutar Covid-19 (coronavirus) a fadin jihar, inda ta ce yanzu ta sassauta zuwa rufe iyakokin jihar kawai.

Janye wannan kudiri na sanya dokar ta baci a jihar, zai baiwa al’ummar jihar damar ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, wadanda tuni suka fara shirin killace kawunansu a gidajensu na tsawon makonni biyu.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar, Shugaban Kwamitin dakile yaduwar cutar Covid-19 a jihar, kuma mataimakin gwamnan jihar, Sanata Baba Tela, ya shaida cewa gwamantin ta yi dogon nazarin halin da jama'a za su fada a sakamakon hana su zirga-zirga da harkokinsu na yau da kullum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel