Gwamnatin Bauchi ta janye dokar hana hana fita a jihar

Gwamnatin Bauchi ta janye dokar hana hana fita a jihar

Gwamnatin jihar Bauchi ta sake waiwaye kan wata sanarwa da ta fitar na sanya dokar ta baci da zata rufe jihar na tsawon kwanaki 14 domin dakile shiga da yaduwar cutar Covid-19 (coronavirus) a fadin jihar, inda ta ce yanzu ta sassauta zuwa rufe iyakokin jihar kawai.

Janye wannan kudiri na sanya dokar ta baci a jihar, zai baiwa al’ummar jihar damar ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, wadanda tuni suka fara shirin killace kawunansu a gidajensu na tsawon makonni biyu.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar, Shugaban Kwamitin dakile yaduwar cutar Covid-19 a jihar, kuma mataimakin gwamnan jihar, Sanata Baba Tela, ya shaida cewa gwamantin ta yi dogon nazarin halin da jama'a za su fada a sakamakon hana su zirga-zirga da harkokinsu na yau da kullum.

Gwamnatin Bauchi Ta janye dokar hana hana fita a jihar

Gwamnatin Bauchi Ta janye dokar hana hana fita a jihar
Source: Twitter

KU KARANTA: Mutane 7 kacal suka halarci daurin auren diyar gwamnan Jigawa (Hotuna)

Wakilin Legit.ng Hausa a jihar Bauchi, ya ruwaito mana cewa a ranar 31 ga watan Maris, gwamnatin jihar ta hannun sakatren gwamnati, Mohammed Sabi’u Baba, ta fitar da snaarwar hana zirga-zirgan na tsawon kwanaki 14 tare da rufe iyakokinta, dokar da zata fara aiki daga karfe shida na yammacin ranar Alhamis.

Mataimakin gwamnan yace, janye dokar ya biyo bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, shuwagabannin addinai dana gargajiya, malaman kiwon lafiya da kuma masu fada a ji a jihar.

Baba Tela ya ce daga yau karfe Shida na yamma dukkanin mashigar jihar za ta kasance a rufe har na tsawon makonni biyu domin kariya daga masu dauko cutar su kawo jihar.

Daga bisani ya bukaci jama'an jihar a harkokinsu na Kasuwanci da sauran harkokin rayuwa da su daina cinkoso domin kiyaye kawunansu daga kamuwa da cutar wacce ta zama babbar annoba da ta addabi kasashen duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel