Labari da dumi-dumi: Tsohon malamin da ya koyar da Abacha, Dr Habibu Gwarzo ya rasu a Kano

Labari da dumi-dumi: Tsohon malamin da ya koyar da Abacha, Dr Habibu Gwarzo ya rasu a Kano

Allah ya yi wa tsohon malamin makaranta kuma daya daga cikin dattijan Kano, Dr Habibu Gwarzo rasuwa yana da shekaru 83 a duniya.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya rasu ne a Asibitin Koyarwa ta Mallam Aminu Kano (AKTH) a ranar Juma'a bayan ya yi fama da rashin lafiya.

An bayyana cewa lokacin yana koyarwa; marigayi Habibu Gwarzo ya koyar da manyan 'yan Najeriya da suka hada da Marigayi Janar Sani Abacha da tsohon shugaban kasa na mulkin soja Ibrahim Badamasi Babangida.

Labari da dumi-dumi: Tsohon malamin Abacha, Dr Habibu Gwarzo ya rasu

Labari da dumi-dumi: Tsohon malamin Abacha, Dr Habibu Gwarzo ya rasu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Covid-19: Sheikh Jingir ya yi wa Lalong biyaya, ya yi sallar Juma'a da mutane kalilan (Hotuna)

Yana daya daga cikin mambobin kwamitin kwararru na sayar da kadarorin gwamnatin tarayya a zamanin mulkin Babangida, ya yi aiki a wasu kwamitoci da wurare da dama.

Ya yi murabus daga koyarwa a shekarar 1965 inda ya koma bangaren kasuwanci kuma ya yi aiki a wurare da dama da suka hada da Kamfanin Hakar Ma'adinai ta Najeriya da ke Jos, Kamfanin Sarrafa Tabar Sigari na Arewa Najeriya da wasu kamfanonin.

A cewar daya daga cikin 'ya'yan shi, Dr Ahmad Tijjani Habibu Gwarzo, mahaifinsu ya dena aikin kamfani ya kafa tasa kamfanin mai suna Jambo International da ya ke kula da ita har zuwa lokacin da ya rasu.

Ya kara da cewa mahaifinsu ya kwashe kimanin shekaru arba'in a rayuwarsa yana ayyukan da'awah addinin islama da wasu ayyukan da suka shafi musulunci.

Marigayi Habibu Gwarzo ya rasu ya bar matar aure guda daya da 'ya'ya takwas kuma tuni an yi ja'izarasa bisa koyarwar addinin musulunci inda aka birne shi a makabartar Tarauni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel