Bidiyo: Bincike zan gabatar a kansu ne - Cewar Fasto da aka kama shi yana tattara kashin mutane

Bidiyo: Bincike zan gabatar a kansu ne - Cewar Fasto da aka kama shi yana tattara kashin mutane

Wani fasto ya ga ta kanshi a hannun mutanen yankin kudu maso yammacin Najeriya, bayan sun iske shi yana tattara kashin mutane yana sanyawa a cikin bakar leda

Da suka sanyo shi a gaba da tambaya, faston ya ce yana so yayi amfani da wannan kashi na mutanen ne ya gabatar da bincike, inda kuma daga baya ya ce yana so yayi amfani da shi ne yayi taki.

Da aka tambayeshi mai yasa bai yi amfani da na 'ya'yansa ko na mutanen da suke zuwa cocinsa ba, sai ya ce: "mutane basa zuwa coci a wannan lokacin." Sai dai wani mutumi a wajen ya ce kamata yayi ya dinga amfani da kashin da mambobin cocinsa suke yi wajen binciken da kuma takin da yace yana so yayi da shi, faston ya sake kare kanshi da cewa a wancan lokacin baya bukatar takin sai yanzu ne amfani shi ya taso.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance:

Mutane suna saurin daukar mataki akan irin wadannan mutanen, musamman yanzu da tsafe-tsafe da asiri yayi yawa a yankin na kudancin Najeriyar.

A wani bangaren kuma mun kawo muku labarin wata mata wacce ta kashe surikarta, inda tace ta aikata hakane domin ta ceci aurenta wanda sirikartar take neman kashe mata.

KU KARANTA: Gwamna Kogi ya dakatar da kwamishinan da ya yiwa budurwa fyade ta karfin tsiya

A wata tattaunawa da Rosemary tayi da jaridar The Nation, ta ce ita da Abaagu Clem sun yi aure ne tun a watan Fabrairun 2016 amma har yanzu babu haihuwa.

Kamar yadda Rosemary ta ce, ita da sirikarta sun kasance makiyan juna tun ranar da Clem ya nuna ta a matsayin wacce yake so ya aura.

Rosemary ta ce sirikarta tayi iyakar kokarinta wajen tabbatar da cewa Clem bai aureta ba amma sai da aka yi auren.

Ta zargi cewa aurenta da Clem yayi ya hana mahaifiyar shi sakat kuma ta sha alwashin tarwatsa auren.

Rosemary ta ce sirikarta ba ta boye kiyayyarta saboda abu kadan ke saka su fada har da dambe.

Kamar yadda ta kara da cewa, rashin haihuwarta kuwa ya kara kawo matsala daga sirikarta don ta fara maganar cewa dan ta zai karo aure. Mijinta kuwa ya fara biyayya ga shawarar mahaifiyar shi don an hada shi da wata yarinya. Wannan kalubalen ne yasa ta halaka sirikar don ba za ta iya jure ganin wata mace tare da mijinta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel