COVID-19: Kwamishinan Lafiya na jihar Enugu ya mutu

COVID-19: Kwamishinan Lafiya na jihar Enugu ya mutu

- Kwamishinan Lafiya na jihar Enugu, Farfesa Anthony Ugochukwu ya rasu

- Ugochukwu ya rasu ne a daren ranar Juma'a 3 ga watan Afrilu a jiharsa ta Enugu

- A cewar Honarabul Jeff Mbah, Kwamishinan bai dade ba da dawo wa Najeriya daga Amurka

A halin yanzu da cutar coronavirus ke yaduwa a wasu jihohin Najeriya, Kwamishinan Lafiya na jihar Enugu, Farfesa Anthony Ugochukwu ya riga mu gidan gaskiya.

Dan majalisar jihar Enugu mai wakiltan mazabar Oji River, Honarabul Jeff Mbah, a ranar Asabar 4 ga watan Afrilun 2020 ne ya sanar da labarin rasuwar Ugochukwu inda ya ce ya rasu a wani asibiti mai suna Memphys Hospital a Enugu kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cewar Honarabul Jeff Mbah, kwamishinan ya dawo ne daga kasar Amurka a baya-bayan nan.

COVID-19: Kwamishinan Lafiya na jihar Enugu ya mutu

COVID-19: Kwamishinan Lafiya na jihar Enugu ya mutu
Source: UGC

DUBA WANNAN: Covid-19: Sheikh Jingir ya yi wa Lalong biyaya, ya yi sallar Juma'a da mutane kalilan (Hotuna)

Mbah ya bayyana rasuwar kwamishinan a matsayin babban rashi ga jihar da ma kasa baki daya.

A cikin bakin ciki, dan majalisar ya ce, "Muna maganan farfesa na Tiyata ne wanda zai iya bayar da muhimmiyar gudun mawa wurin kawo gyara a fanin lafiya a kasar mu. Wannan babban rashi ne."

Har wa yau, Legit.ng ta ruwaito cewa hukumar NCDC a ranar Juma'a 27 ga watan Maris ta tabbatar da mutum biyu sun kamu da coronavirus a jihar Enugu.

Wannan shine karo na farko da aka samu bullar cutar a yankin Kudu maso gabashin kasar.

Legit.ng ta gano cewa ma'aikatan lafiya na jihar ta Enugu ta ce mutane da kansu ne suka neman ayi masa gwajin na coronavirus bayan sun dawo daga kasar Birtaniya.

Gwamnatin na jihar Enugu ta mika godiyarta ga mutanen da suka kai kansu ma'aikatar lafiyar bayan an sanar da cewa duk wadanda suka dawo daga kasashen waje su tafi domin a duba su.

Gwamnatin ta shawarci dukkan wadanda suka dawo daga kasashen waje su kira lambobin waya kamar haka 08182555550 or 09022333833.

Ta kuma yi kira ga al'umma su kwantar da hankulansu domin gwamnatin tana daukan dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da cutar ba ta yadu a jihar ba kana ta shawarci mutane su cigaba da bin shawarwarin likitoci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel