NCDC ta yi kuskure a sanar da jimillar masu COVID-19 a Najeriya, ta yi gyara

NCDC ta yi kuskure a sanar da jimillar masu COVID-19 a Najeriya, ta yi gyara

Hukumar Kare Cutattuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce ta yi kuskure wurin sanar da sakamakon gwajin COVID-19 a kasar.

"A ranar 3 ga watan Afrilun 2020, mun ruwaito cewa an samu karin sabbin masu dauke da COVID-19 a Najeriya," Kamar yadda NCDC ta wallafa a shafin ta na Twitter. "An gano kuskure a cikin wannan sanarwar kamar haka:

"Karin sabbin wadanda suka kamu da Covid-19 guda 25 ne aka samu a Najeriya. Na 26 da aka lissafa maimaci ne na wani da ya kamu da cutar da aka yi wa gwaji tun a baya, ba sabo bane.

"A cikin sabbin mutane 25 da aka ruwaito sun kamu da cutar, An yi kuskuren ruwaito daya daga jihar Osun. Ainihi daga jihar Oyo ne, ainihin kididdigan wadanda suka kamu da cutar a jihohin Najeriya shine: Legas - 11, Osun - 6, Abuja - 3, Edo - 3 Ondo - 1, Oyo - 1."

DUBA WANNAN: Covid-19: Sheikh Jingir ya yi wa Lalong biyaya, ya yi sallar Juma'a da mutane kalilan (Hotuna)

A cewar hukumar ta NCDC, a misalin karfe 10.30 na daren ranar 3 ga watan Afrilu an samu mutum 209 da suka kamu da kwayar cutar, mutum hudu sun mutu sannan mutum 25 sun warke.

"Muna neman afuwar kuskuren da muka yi wurin sanar da adadin sabbin mutanen da suka kamu da Covid-19 a Najeriya a jiya," a cewar hukumar.

"Hukumar NCDC za ta cigaba da ba wa 'yan kasa sahihin rahoto kan halin da ake ciki game da yaduwar cutar a Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel