Magidanci ya bayyana cewa iyalinsa duka sun kamu da Coronavirus ciki har da 'ya'yansa guda 11

Magidanci ya bayyana cewa iyalinsa duka sun kamu da Coronavirus ciki har da 'ya'yansa guda 11

- An samu iyalan mutum daya har su 12 a gida daya dauke da muguwar cutar coronavirus a kasar Spain

- Mahaifiyar da yaranta 11 duk sun bayyana dauke da kwayar cutar wacce ta kama mutane a kalla 117,000 a kasar Spain

- Suna karkashin doka mai tsauri ta killace kansu wacce saboda hakan yasa yaran suke daukar darussan makaranta ta na'ura mai kwakwalwa

Iyalan mutum daya a kasar Spain wadanda suka hada da matar shi da yara 11 duk sun kamu da muguwar cutar coronavirus.

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito, An tirsasa iyalan killace kansu ne a gidansu bayan an gano dukkansu na dauke da muguwar cutar coronavirus.

Magidanci ya bayyana cewa iyalinsa duka sun kamu da Coronavirus ciki har da 'ya'yansa guda 11
Magidanci ya bayyana cewa iyalinsa duka sun kamu da Coronavirus ciki har da 'ya'yansa guda 11
Asali: Facebook

Mahaifiyar mai suna Irene Gervas ce wacce aka fara samu da cutar kafin mijinta mai suna Jose Mafia Cebrian a tabbatar da nashi. Yaransu 11 masu suna Carmen mai shekaru 15, Fernando mai shekaru 14, Luiz mai shekaru 12, Juan Pablo mai shekaru 12, tagwaye Miguel da Manuel masu shekaru 10, Alvaro mai shekaru 8, Irene mai shekaru 5, Alicia mai shekaru 4, Helena mai shekaru 3 sai kuma Maria mai shekara daya duk an gano suna dauke da muguwar cutar.

Mahaifin mai suna Jose Maria Cebrian ya sanar da manema labarai cewa: "Yaran sun fara zazzabi ne daya bayan daya. Wasu na warkewa, wasu na farawa. A yayin da cutar ta kai kwanaki biyar zuwa shida, sai mu fara zargi amma kuma sai su warke."

"A nan dai, yaran sun fara da ciwon kai ne da amai. Bayan amai sai suka fara samun lafiya. Sai kuma lafiya ta samu." Yace.

KU KARANTA: Zamu kara kwanakin hana zirga-zirga idan har baku kama kanku ba - Gargadin Lai Mohammed ga 'Yan Najeriya

Tun da aka gwada su a ranar 14 ga watan Maris, dukkan 'yan gidan an sa musu tsauraran dokokin killace kansu sannan an hana kowa ziyartar su don kada a kwashi kwayar cutar.

Cebrian ya kara da cewa: "Likita ya ce a kalla mu dau makonni biyu a killace saboda cutar da muke da ita. Idan muka fita za mu iya yada cutar."

Kamar yadda ya ce, dan su kadai aka amince ya je siyo musu magani amma sanye da takunkumin fuska da kuma safar hannu.

Cebrian ya kara da cewa: "Shi kadai yake fita kadan. Idan aka kawo mana kayan abincinmu, ana ajiyesu ne a gareji sai ya je ya dauko."

Yaran na karatu daga gida ne ta hanyar amfani da na'ura mai kwakwalwa da wayoyin hannu.

Jose Maria ya ce: "Akwai matukar amfani killace kanmu da muke yi. Amma yaran na karatu a na'ura mai kwakwalwa da wayoyin hannu daga Litinin zuwa Juma'a."

A halin yanzu dai kasar Spain na da mutane a kalla 117,000 masu cutar sannan mutane kusan 11,000 ne suka rasa rayukansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel