Zamu kara kwanakin hana zirga-zirga idan har baku kama kanku ba - Gargadin Lai Mohammed ga 'Yan Najeriya

Zamu kara kwanakin hana zirga-zirga idan har baku kama kanku ba - Gargadin Lai Mohammed ga 'Yan Najeriya

- Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kiyaye dokar hana walwala da shugaban kasa ya saka

- Kamar yadda Lai Mohammed ya sanar, rashin bin dokar nan zai iya sa shugaban kasan ya kara wasu makonni biyun bayan wanda ya sa sun kare

- Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su guji taruka sannan a dage wajen tsaftace jiki gudun yaduwar muguwar cutar coronavirus

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya ja kunnen 'yan Najeriya a kan dokar hana walwala da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka a ranar 29 ga watan Maris. Ya ce za a kara kwanaki matukar 'yan Najeriya ba su kama kansu ba.

Ministan ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da kwamitin shugaban kasan na yaki da cutar coronavirus yayi a Abuja a ranar Juma'a, 3 ga watan Afirilu.

Zamu kara kwanakin hana zirga-zirga idan har baku kama kanku ba - Gargadin Lai Mohammed ga 'Yan Najeriya
Zamu kara kwanakin hana zirga-zirga idan har baku kama kanku ba - Gargadin Lai Mohammed ga 'Yan Najeriya
Asali: UGC

Lai Mohammed ya yi kira ga 'yan Najeriya da su guji hada taruka kuma a dinga tsaftace jiki. Ta hakan ne kadai kowa zai koma al'amuran shi hankali kwance nan da kwanaki 14.

KU KARANTA: Magidanta sun kashe kansu da adduna akan budurwar da suka shafe shekara 2 suna so

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito, Lai Mohammed ya ce: "Idan bamu kama kanmu ba, akwai yuwuwar a kara kwanakin dokar hana walwalar. Amma idan mun kama kanmu, ba dole bane a kara amma muna fatan hakan.

"Idan muka zauna gida na makonni biyu kuma muna hana yaduwar cutar, komai zai wuce.

"A don haka ne nake kira ga 'yan Najeriya da su yi duk abinda ya dace na kiyaye dokokin kauracewa taro da kuma tsafta. Bayan makonni biyu, kowa zai koma lamurran shi.

"Amma idan suna tunanin wasa ne, toh bamu da zabin da ya wuce mu saka kowa zaman gida na karin wasu makonni biyun."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: