Covid-19: Najeriya ba ta cikin kasashen da Bankin Duniya za ta ba tallafi

Covid-19: Najeriya ba ta cikin kasashen da Bankin Duniya za ta ba tallafi

An ware Najeriya daga cikin jerin kasashe na farko da za su fara amfana da tallafin gaggawa da Bankin Duniya za ta bawa kasashe masu tasowa domin taimaka musu wurin yaki da yaduwar annobar cutar coronavirus a kasashen su.

An kaddamar da shirin bayar da tallafin Covid-19 din ne a ranar Alhamis bayan samun amincewar kwamitin direktocin Bankin Duniya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Abin mamaki dai babu sunan Najeriya a cikin jerin kasashen da za su amfana da tallafin kamar yadda Bankin Duniyar ta wallafa a shafin ta na Intanet duk da cewa Najeriya tana daga cikin kasashe masu tasowa da cutar ta yi wa illa.

Covid-19: Bankin Duniya ta cire Najeriya cikin kasashen da za su fara samun tallafi
Covid-19: Bankin Duniya ta cire Najeriya cikin kasashen da za su fara samun tallafi
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Covid-19: Sheikh Jingir ya yi wa Lalong biyaya, ya yi sallar Juma'a da mutane kalilan (Hotuna)

Bullar annobar ta coronavirus ya janyo faduwar darajar kudin danyen man fetur a kasuwannin duniya kuma man fetur din shi ne abinda kasar ta fi dogara da shi wurin samun kudaden shiga.

Kazalika, adadin mutane masu dauke da kwayar cutar yana karuwa kullum a kasar inda a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020 akwai mutane kimanin 200 da aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar.

Ana fargabar cewa asibitocin da ke kasar ba za su iya kulawa mutanen da za su bukaci magunguna ba idan annobar ta cigaba da yaduwa kuma a ranar Alhamis gwamnatin kasar ta roki attajirin kasar Amurka Elon Musk ya taimaka mata da na'urar numfashi duk da cewa daga baya ta janye rokon.

Kasashe guda 25 ne aka lissafa a jerin kasashen da za su amfana da tallafin na Covid-19 inda za a kashe kudi kimanin Dalla Biliyan 1.9.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel