Yanzu-yanzu: Masu cutar Coronavirus 6 sun gudu da inda aka killacesu a Osun
Gwamnatin jihar Osun ta alanta neman mutane shida masu cutar Coronavirus ruwa a jallo bayan sun gudu daga inda aka killacesu a Ejigbo, jihar Osun ranar Juma'a.
Mutanen na cikin tawagar matafiyan da suke shigo Najeriya daga kasar Cote d'ivoire a makon da ya gabata kuma aka samesu da cutar ta COVID-19.
A lokacin gwamnatin jihar ta killacesu a kauyen Ejigbo.
Wani jawabi daga gwamnatin jihar ya bayyana sunayen mutane shidan da lambar wayarsu.
KU KARANTA: An gano mai coronavirus da ya tsere daga asibiti a Osun

Asali: Twitter
A bangare guda, Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane ashirin (20) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Juma'a, 3 ga Afrilu, 2020.
Hukumar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita ranar Juma'a inda tace: “An tabbatar da mutane ashirin (20) sun kamu da #COVID19 a Najerya, 11 a Legas, 3 a Abuja, 3 a Edo, 2 a Osun, 1 a Ondo.“
"An samu karin mutane biyu da mutu; 1 a Legas, 1 a Edo."
“Dai-dai Karfe 10:30 na daren 3 ga Afrilu, mutane 210 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami 25 , kuma hudu ya rigamu gidan gaskiya.“
Lagos- 109
Abuja - 41
Osun- 21
Oyo- 8
Akwa Ibom- 5
Ogun- 4
Edo- 6
Kaduna- 4
Bauchi- 3
Enugu- 2
Ekiti- 2
Rivers-1
Benue- 1
Ondo - 1
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng